Peter Obi Zai Shafe Makonni Yana Gabatar da Shaidu a Gaban Kotu
- Kotun zabe a Najeriya ta ware wa Peter Obi da Labour Party mako uku su gabatar da shaidun da yasa su ke kalubalantar nasarar Tinubu
- Mai shari'a Haruna Tsammani ya ce Kotu ta yanke baiwa Obi mako 3 ne saboda ƙarancin lokaci
- Obi ta bakin lauyansa ya nemi a ba shi mako Bakwai domin tabbatar da cewa ba Tinubu ne ya samu nasara a zaben 2023 ba
Abuja - Kotun sauraron ƙararrakin zaben shugaban ƙasa ta umarci Peter Obi da jam'iyyar Labour Party su haɗu su gabatar da ƙorafe-korafensu cikin makonni uku.
Punch ta rahoto cewa Obi zai gabatar da duk wani korafinsa da shaidu game da nasarar Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, a gaban Kotun cikin wannan wa'adi da aka ware masa.
A ɗaya bangaren kuma, Kotun zaben ta umarci zababben shugaban ƙasa, Bola Tinubu, ya kare nasarar da ya samu a babban zaben 2023 tare da hukumar zaɓe INEC cikin kwanaki 5.
Shugaban kwamitin alƙalan Kotun zabe a Najeriya, Mai shari'a Haruna Tsammani ne ya sanar da haka yayin gabatar da rahoton zaman sharar fagen da ya gabata.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Daga cikin abubuwan da ya gabatar, Mai shari'a Tsammani ya umarci Obi ya fara gabatar da shaidu da ƙorafinsa kan zaben shugaban ƙasa daga ranar 30 ga watan Mayu zuwa 23 ga watan Yuni, 2023.
Idan baku manta ba, Obi ta bakin lauyansa, Farfesa Awa Kalu, SAN, ya roƙi a ba shi tsawon makonni 7 domin gabatar da tuhumar da yake kan nasarar Tinubu, inji rahoton Vanguard.
Sai dai Kotun zaben ta bayyana cewa ta yanke hukuncin ware wa Obi mako uku saboda ƙarancin lokacin da take da shi domin ƙarƙare zaman shari'ar baki ɗaya.
Haka zalika Kotun ta umarci haɗa baki ɗaya kararrakin da aka shigar na kalubalantar sakamakon zaɓen shugaban ƙasa wuri ɗaya domin a yi hanzarin karkare sauraron ƙarar.
Sannan mai shari'a Tsammani ya yi fatali da jayayyar Tinubu da jam'iyyar APC, wanda suka nuna adawa da yunkurin cure ƙararrakin wuri ɗaya.
Buhari ya tura takarda ga majalisar dattawa
A wani labarin kun ji cewa Shugaba Buhari Ya Nemi Majalisa Ta Amince Ya Maida Wa Gwamnatin Borno Biliyan N16bn.
A wata wasiƙa da ya aike wa majalisar dattawa, shugaban ƙasan ya ce kuɗin na wasu ayyukan FG ne da gwamnatin Borno ta gudanar da aljihunta.
Asali: Legit.ng