Manyan Jiga-Jigan PDP Da Magoya Bayan Jam’iyyar Sun Sauya Sheka Zuwa APC a Ondo

Manyan Jiga-Jigan PDP Da Magoya Bayan Jam’iyyar Sun Sauya Sheka Zuwa APC a Ondo

  • Babbar jam'iyyar adawa ta PDP ta rasa wasu manyan jiga-jiganta inda suka koma jam'iyyar APC mai mulki a jihar Ondo
  • Shugabannin jam'iyyar da dubban magoya bayan PDP sun sauya sheka zuwa jam'iyyar All Progressives Congress (APC)
  • Masu sauya shekar sun bayyana rikcin shugabanci a PDP a matsayin dalilinsu na barin jam'iyyar a jihar Ondo

Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Ondo ta rasa manyan jiga-jiganta inda suka koma jam'iyya mai mulki a jihar.

Dubban mambobin jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Ondo ciki harda dan takarar kujerar dan majalisar wakilai, Olumuyiwa Adu, sun sauya sheka zuwa jam'iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki a ranar Litinin, 22 ga watan Mayu.

Shugabannin PDP da APC
Manyan Jiga-Jigan PDP Da Magoya Bayan Jam’iyyar Sun Sauya Sheka Zuwa APC a Ondo Hoto:Umar Illiya Damagum, Abdullahi Adamu
Asali: Facebook

Shugabannin PDP sun sauya sheka

Hakazalika, shugaban PDP a Akokoland, Bode Obanla, ya jagoranci masu sauya sheka daga kananan hukumomi hudu a yankin Akoko ta kudu maso yamma, Akoko ta kudu maso gaban, Akoko ta arewa maso yamma da Akoko ta arewa maso gabas, rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-ɗumi: Tsohon Shugaban PDP da Wasu Jiga-Jigai Sun Kara Rikita Jam'iyyar

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Dalilin da yasa shugabannin PDP suka sauya sheka zuwa APC

Da yake jawabi kan ci gaban, Adu ya ce ya yanke shawarar barin PDP tare da mabiyansa ne saboda rikicin shugabanci a jam'iyyar, Nigerian Tribune ta rahoto.

Dan siyasar ya kuma bayyana cewa jam'iyyar ta rasa alkibla a lamuranta.

Zan yi koyi da Umaru Musa Yar'adua idan na karbi mulki, Tinubu

A wani labari na daban, shugaban kasar Najeriya mai jiran gado, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya sha alwashin yin koyi da marigayi tsohon shugaban kasa Umaru Musa Yar'adua idan ya karbi mulki a ranar 29 ga watan Mayu.

Bola Tinubu ya bayyana marigayi Yar'adu a matsayin jajirtaccen shugaban nagari wanda babu abun da ya sanya a gaba face ci gaban kasar da kuma tabbatar da mulkin damokradiyya.

Zababben shugaban kasar ya bayyana hakan ne a cikin sakon jinjina da ya saki a ranar Juma'a, 5 ga watan Mayu wanda ya yi daidai da cikar marigayi tsohon shugaban kasar Najeriyan shekaru goma sha uku da barin duniya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng