Rashin Tsaro Ya Hana Bacci Ga Mugayan Mafarkai a Lokacin Mulki Na, Jonathan
- Goodluck Jonathan ya ce matsalar tsaro ta hana shi bacci, ta zama masa alaƙaƙai a lokacin yana kan kujerarar shugaban ƙasa
- Tsohon shugaban ƙasan ya ce yadda ya ga rana haka yake ganin dare a kokarin dawo da zaman lafiya a sassan ƙasar nan
- Ya yi wannan jawabi ne yayin kaddamar da muhimmin aikin da gwamnan Taraba ya kammala mako biyu gabanin ya sauka
Taraba - Tsohon shugaban ƙasa, Dakta Goodluck Ebele Jonathan, ya ce matsalar tsaro ce babban abinda ya fi muni da ke hana shi bacci a zamanin mulkinsa tsakanin 2010 zuwa 2015.
Channels tv ta rahoto cewa Jonathan ya bayyana haka a wurin kaddamar da babban titi mai tsawon kilomita 22 a jihar Taraba, Arewa maso Gaɓashin Najeriya.
Yayin yaba wa gwamna Darius Ishaku kan ayyukan alherin da ya zuba wa mutanen jiharsa, Jonathan ya ce babban ƙalubalen da ya sa shi mafarkai mara daɗi lokacin yana kan gadon mulki shi ne rashin tsaro.
Ya ce a lokacin ba ya iya kwanciya ya yi bacci duk a kokarin ganin mutane sun samu zaman lafiya domin ta haka ne kaɗai za'a samu ci gaba a ƙasar nan.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Bayan kaddamar da titin mai hannu biyu, Jonathan ya wuce wurin buɗe fara aikin gina babbar tsahar aje manyan Motoci a Jalingo, ya jaddada cewa zaman lafiya na hannun al'umma.
Tsohon shugaban ƙasa ya nuna gamsuwarsa ganin yadda jihar Taraba ta fara komawa tamkar kyawawan lokutan baya na zaman lafiya da haƙuri da juna.
Abinda ya sa muke gina tituna - Ishaku
A nasa jawabin, Gwamna Ishaku ya ce gwamnatinsa ta rungumi gina tituna ne domin haɗa yankunan karkara da cikin birni na nufin hakan ya ƙara fito aikin gona a jihar.
Wannan na zuwa ne ƙasa da mako biyu gabanin rantsar da sabuwar gwamnati a jihar Taraba ranar 29 ga watan Mayu, 2023, kamar yadda This Day ta rahoto.
Sarkin Musulmai ya ja hankalin yan Najeriya
A wani labarin kuma Mai Alfarma Sarkin Musulmai ya bukaci baki ɗaya yan Najeriya sun jingine kowane irin banbanci su marawa gwamnatin Tinubu baya.
Sultan ya ce an shafe dogon lokaci fararen hula ke mulki a Najeriya tum 1999, ya kamata kowa ya maida wuƙarsa kube ya sanya kishin ƙasa a gaba.
Asali: Legit.ng