Wase: Har Yanzun Ina Cikin Tseren Kujerar Kakakin Majalisar Wakilai
- Ɗan majalisar tarayya daga jihar Borno, Ahmed Wase, ya ce har yanzun yana cikin tseren neman zama kakakin majalisa ta 10
- Wase, mataimakin kakaki a majalisa ta 9, ya ce bai janye ba kuma bai hakura ya koma bayan kowane ɗan takara ba
- Ya bayyana haka ne a fadar shugaban kasa jim kaɗan bayan ganawa da shugaba Muhammadu Buhari a Abuja
Abuja - Mataimakin kakakin majalisar wakilan tarayya, Honorabul Idris Ahmad Wase, ya jaddada cewa zai ci gaba da ƙoƙarin cika burinsa na zama kakakin majalisa na gaba.
Rahoton The Nation ya nuna cewa Honorabul Wase ya bayyana haka ne yayin hira da yan jarida a fadar shugaban ƙasa jim kaɗan bayan ganawa da shugaba Muhammadu Buhari.
Haka nan kuma ɗan majalisar ya yi fatali da raɗe-raɗin da ke yawo cewa ya amince ya hakura da takara domin marawa Honorabul Tajudeen Abbas baya, wanda APC ta zaɓa.
A jawabinsa, Wase ya ce:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Ina nan a cikin tseren 'yan takara kuma idan Allah ya yarda ni zan karkare wannan tseren. Ban janye daga takara ko na hakura na koma bayan kowa ba."
Wase ya ƙara da cewa takardan kason kujerun majalisar da kwamitin gudanarwa na jam'iyyar APC ta ƙasa (NWC) ya aiko, ta ba da damar a ci gaba da tattauna wa kan batun.
"Ba ina magana a madadin ni karan kaina bane, a baya kun hana mu mataimakin shugaban majalisar dattawa sannan kuka bamu mataimakin kakakin majalisa."
"Yanzu kuma ba zai yuwu ku wurgad damu a juji ba duk da kowa ya san cewa mun tabuka abun a zo a gani a ɓangaren yawan kuri'u da goyon bayan gwamnati.
- Ahmed Wase
Wase na ɗaya daga cikin 'yan takarar kakakin majalisa ta suka lashi takobin yaƙar ɗan takarar da zababben shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, da APC suke goyon baya, The Cable ta rahoto.
"Ba Zamu Yi Sa'insa da Kai Ba," EFCC Ta Maida Martani Ga Gwamna Matawalle
A wani labarin kuma kun ji cewa EFCC Ta Maida Zazzafan Martani Ga Gwamnan Matawalle Kan Zargin Cin Hanci.
EFCC ta maida martani ga Matawalle, ta ce ba zata tsaya sa'insa da wanda take tuhuma da wawure kuɗin talakawa ba.
Alaƙa ta ƙara tsami tsakanin EFCC da Matawalle tun bayan da hukumar ta zargi gwamnan da karkatar da N70bn.
Asali: Legit.ng