Kotu Ta Musanta Soke Tikitin Takarar Zababben Gwamnan Jihar Abia
- Babbar kotun tarayya mai zamanta a birnin Kano, ta musanta soke tikitin takarar zaɓaɓɓen gwamnan jihar Abia, Dr Alex Otti
- Kotun ta bayyana cewa ba a shigar da ƙara a gabanta kan ƴan takarar jam'iyyar Labour Party na jihar Abia ba
- Sai dai babbar kotun tarayyar ta soke zaɓen fidda gwani wanda jam'iyyar Labour Party ta gudanar a jihar Kano
Jihar Kano - Wata babbar kotun tarayya a birnin Kano, ta musanta soke halascin takarar zaɓaɓɓen gwamnan jihar Abia, Dr Dr Alex Otti.
Sai dai, kotun tace ta soke zaɓen ƴan takarar jam'iyyar Labour Party a jihar Kano, da suka fafata a babban zaɓen 2023, rahoton The Punch ya tabbatar.
Wani mai shigar da ƙara, Mr Ibrahim Haruna-Ibrahim, ya shigar da ƙara yana neman kotun ta soke dukkanin satifiket ɗin cin zaɓe da aka ba ƴan takarar jam'iyyar Labour Party, da suka samu nasara a jihar Kano da sauran jihohi 35 haɗi da birnin tarayya Abuja.
Waɗanda ake ƙara a cikin ƙarar su ne jam'iyyar Labour Party da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC).
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Alƙalin kotun, mai shari'a Muhammad Nasir-Yunusa, ya ce ƴan takarar da suka fafata a babban zaɓen 2023 a jihar Abia, ba a shigar da su ƙara a gaban kotun sa ba, cewar rahoton Vanguard.
"Wannan kotun ba ta da hurumin bayar da umurni kan satifiket cin zaɓe. Suna da hurumin neman haƙƙinsu a kotun da ta dace." A cewarsa.
Ya bayyana cewa hukumar INEC tana da hurumin amsar rajistar sunayen mambobin jam'iyyar Labour Party da sauran jam'iyyu, kwanaki 30 kafin yin zaɓen fidda gwani domin bin umurnin sashi na 77(3) na sabuwar dokar zaɓen 2022.
Sashin ya bayyana cewa duk jam'iyyar da ba ta bi ƙa'idar sashi na 77(2)(3) na sabuwar dokar zaɓen 2022 ba, ba za a iya ayyana ta a matsayin wacce ta lashe zaɓe ba.
"Wannan kotun ta soke zaɓen fidda gwanin jam'iyyar Labour Party a jihar Kano." A cewar alƙalin.
Dalilan Da Za Su Wargaza Hukuncin Kotu Kan Nasarar Alex Otti
A wani labarin na daban kuma, kun ji cewa wani fitaccen lauya ya yi bayani kan wasu ƙwararan dalilai shida da za su sanya hukuncin kotu kan zaɓen zaɓaɓɓen gwamnan jihar Abia, Alex Otti, ya wargaje.
Lauyan ya bayyana cewa an shigar da ƙarar ne bayan an kwashe wata ɗaya da bayyana Alex Otti a matsayin wanda ya yi nasara a zaɓen.
Asali: Legit.ng