Majalisa Ta 10: Gbajabiamila Ya Gargadi Masu Son Kawo Cikas a Majalisun Tarayya da Su Guji Fushin Tinubu

Majalisa Ta 10: Gbajabiamila Ya Gargadi Masu Son Kawo Cikas a Majalisun Tarayya da Su Guji Fushin Tinubu

  • Shugaban majalisar wakilai ya gargadi masu son kawo cikas a majalisun tarayya da su guji fushin Tinubu
  • Femi ya yi wannan gargadin ne a wani taron da zababbun ‘yan majalisun tarayya suka yi a Transcorp Hilton Otal
  • Ya ce gwamnatin tsohon shugaba Jonathan ta hukunta su akan bijirewar da suka yi wa gwamnatin a baya

Abuja - Shugaban majalisar wakilai ta Najeriya Femi Gbajabiamila ya gargadi masu son kawo cikas akan shugabancin majalisun tarayya da su guji bacin ran zababben shugaban kasa Bola Tinubu.

Gbajabiamila ya yi wannan gargadi ne a wani taro da zababbun ‘yan majalisu suka yi a Transcorp Hilton otal a Abuja a ranar Laraba 17 ga watan Mayu.

Gbajabiamila/Abbas/Akpabio
Gbajabiamila Ya Gargadi Masu Son Kawo Cikas a Majalisun Tarayya. Hoto: Premium Times
Asali: Facebook

Jam’iyya mai mulki ta APC da kuma Bola Tinubu sun zabi Godswill Akpabio a matsayin shugaban majalisar dattawa yayin da Abbas Tajudden aka zabe shi a matsayin shugaban majalisar wakilai.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Gbajabiamila Ya Ce Ya Yi Nadamar Goyon Bayan Tambuwal Da Ya Yi Ya Zama Kakakin Majalisa

Gbajabiamila ya yi dana sanin marawa Tambuwal baya

Gbajabiamila ya gargadi sabbin zababbun ‘yan majalisar akan bijirewa umarnin jam’iyya inda ya ce ya yi dana sanin marawa Aminu Tambuwal baya a matsayin shugaban majalisar a shekarar 2011.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya kara da cewa yana tuna irin bijirewa shugaba Jonathan da suka yi a wancan lokacin saboda shugaban ya koya musu hankali a sanadin bijirewarsu ga umarninsa, jaridar Premium Times ta tattaro.

Gbajabiamila ya ce a lokacin shi ne shugaban marasa rinjaye a majalisar ta 7 wanda yana gaba-gaba wajen goyon bayan Tambuwal da bjirewa jam’iyya mai mulki da ta zabi Mulikat Akande a wancan lokaci

A cewarsa:

“Nine na jagoranci bijirewa jam’iyya mai mulki da goyon bayan Tambuwal a matsayin shugaban majalisa, wanda har yau ina dana sanin wannan abu.”

Wasu matakai aka dauka don hukunta su?

Kara karanta wannan

Ku Cika Alkawuran Da Kuka Dauka Ko A Yi Waje Da Ku, Buhari Ya Shawarci Gwamnoni

Rahotanni sun tattaro cewa Gbajabiamila ya umarci Abbas wanda yana daga cikin wanda lamarin ya faru dasu da ya yi bayanin irin matakin da tsohon shugaba Jonathan ya dauka don hukunta su.

Gbajabiamila ya kara da cewa:

“Shugaban majalisa mai jiran gado zai fada muku wahalar da muka a wancan lokacin har na tsawon shekaru 4.”

Honarabul Abbas ya yi bayanin matakin da Jonathan ya dauka a kansu

Da yake bayani akan abubuwan da suka faru a dalilin bijirewa da suka yi, Abbas Tajudden ya ce:

“Jam’iyyar PDP ta zabi Mulikat Akande a matsayin shugabar majalisar, amma muka bijire saboda mu komai na gwamnati mai kyau ko marar kyau muna adawa da shi, muka bijire muka zabi Tambuwal.
“Bayan makwanni biyu da zaban Tambuwal, abu na farko da muka fara fiskanta shi ne an rage kudin mazabu da ake bayarwa, kuma 50% zamu samu daga alawus na aiki.”

Kara karanta wannan

'Dan Shugaba Obasanjo Ya Fadi Wadanda Suka Dace da Shugabancin Majalisar Tarayya

Ku biya bukatunku tunda kun bijirewa gwamnati

Honarabul Abbas ya ce:

“Tunda kuka zabi ku ci mutuncin wannan gwamnati, ku biya wa kanku bukatu, ku samu shugaban majalisar da kuka zaba, haka muka biya bashin da majalisa ta 6 ta bari har na tsawon shekara daya.
“Sannan ayyukan yanki wanda ko wane dan majalisa ke da shi a karshen shekara an rage shi zuwa 30%, idan kana daukar N100m a matsayin kudin ayyukan mazabarka, N30m kawai zaka samu, wannan shi ne hukuncin da aka mana.”

Gbajabiamila ya Bayyana Abin da Ya Jawowa Manyan ‘Yan Majalisa Rasa Kujerunsu

A wani labarin, shugaban majalisar wakilai ta Najeriya ya bayyana dalilan da suka jawo faduwar 'yan majalisa da dama.

Ya ce amfani da addini da bangaranci shi ne babban abin da jawo faduwar jiga-jigan majalisar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.