Batun Karbar N500m, Shugaban Tsagin Jam'iyyar Labour Party Ya Bayyana Gaskiya

Batun Karbar N500m, Shugaban Tsagin Jam'iyyar Labour Party Ya Bayyana Gaskiya

  • Gaskiya ta fito dangane da batun cika aljihun shugaban tsagin jam'iyyar Labour Party, Lamidi Apapa, da N500m
  • Apapa ya fito fili ya musanta cewa ya ƙarbi waɗannan kuɗin domin haddasa fitina a jam'iyyar Labour Party
  • Shugaban jam'iyyar ya kuma buƙaci Peter Obi, da ya sanya baki domin kawo ƙarshen rikicin shugabancin jam'iyyar da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa

Abuja - Shugaban tsagin jam'iyyar Labour Party, Lamidi Apapa, ya musanta zargin ƙarbar N500m domin kawo cikas ga ƙarar da jam'iyyar ta shigar a kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa.

Apapa ya kuma buƙaci ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar, Peter Obi, a zaɓen ranar 25 ga watan Fabrairru, da ya sanya bakin kan rikicin shugabancin jam'iyyar, domin kawo ƙarshensa, cewar rahoton Daily Trust.

Lamidi Apapa ya musanta karbar N500m
Lamidi Apapa yayin ganawa da manema labarai Hoto: Vanguard.com
Asali: UGC

Da ya ke magana da manema labarai, bayan ya sha da ƙyar a hannun fusatattun matasa a kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa, ranar Laraba a birnin tarayya Abuja, Apapa ya musanta cewa ya ƙarbi kuɗi da batun wani ko wasu ne ke ingiza shi ya ke ƙoƙarin yi wa jam'iyyar zagon ƙasa.

Kara karanta wannan

Labour Da Peter Obi Sun Gaza Biyan N1.5m Don Karɓar Takardun Da Kotu Ke Nema, INEC

Ya bayyana cewa dole ne Peter Obi, ya cire son rai ya sanya idon basira wajen magance rikicin domin shawo kan matsalar shugabancin jam'iyyar, rahoton The Guardian ya tabbatar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Lamidi ya bayyana laifin Peter Obi

Lamidi ya ce da tuni an manta da rikicin shugabancin jam'iyyar, da ace Peter Obi ya mutunta umurnin babbar kotun tarayya da ke a birnin tarayya Abuja.

Babbar kotun tarayya a Abuja, ta umurci Julius Abure da wasu mutum uku daga kiran kan su a matsayin shugabannin jam'iyyar, bisa samun su dumu-dumu da laifi.

Ya ce kuskure ne Obi ya riƙa mutunta Abure, bayan hukuncin da kotun ta yi, a matsayinsa na ɗan takarar shugaban ƙasa, wanda ya ke neman a yi masa adalci a gaban kotu.

Labour da Peter Obi Sun Gaza Biyan N1.5m

Kara karanta wannan

Rigima Sabuwa: Shugaban Tsagin Jam'iyyar Labour Party Ya Sha Da Kyar a Kotun Zabe, Bidiyon Ya Bayyana

A wani labarin na daban kuma, hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC), ta gayawa kotu cewa kotu cewa jam'iyyar Labour Party gaza biyan kuɗin da ake buƙata domin ƙarɓar takardun da kotu ta ke nema.

Lauyan INEC a kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa, ya gayawa kotun cewa jam'iyyar ta kasa biyan N1.5m domin amsar takardun.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng