Ni Ba Karamin Jarumi Bane, Gwamna Ayade Ya Yaba Wa Kansa

Ni Ba Karamin Jarumi Bane, Gwamna Ayade Ya Yaba Wa Kansa

  • Gwamna Ben Ayade na jihar Kuros Riba ya ayyana kansa a matsayin Jarumi saboda biyan ma'aikata da yan fansho hakkinsu
  • Farfesa Ayade ya ce jiharsa ce ta ɗaya a biyan ma'aikata albashi amma ita ce ta 36 a samun kuɗin shiga daga FG
  • Ya ce duba da babban gibin da ake samu tsakanin kuɗin da yake biya a matsayin albashi da kason jiharsa, ya cancanci a yaba masa

Cross River - Gwamnan jihar Kuros Riba, Farfesa Ben Ayade, ya ce kokarin da gwamnatinsa ta yi na biyan ma'aikata albashi da biyan 'yan fansho abu ne mai kyau da ya cancanci yabo.

A wata hira da Ariae TV ranar Laraba, gwamna Ayade, mamban jam'iyyar APC, ya ayyana kansa da, "Gwarzon jarumi," kana ya ƙara da cewa talakawa suna jinjina masa kan nasarorin da ya samu.

Kara karanta wannan

Rai Ya Yi Halinsa Yayin Da Fada Ta Barke a Tsakanin Jami'an EFCC a Sokoto

Ben Ayade.
Ni Ba Karamin Jarumi Bane, Gwamna Ayade Ya Yaba Wa Kansa Hoto: dailytrust
Asali: Facebook

A cewarsa, biyan ma'aikata albashi da kuma biyan 'yan fansho hakkokinsu ya fi muhimmanci fiye da ko wane irin aiki a wurinsa, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Gwamna Ayade ya yi ikirarin cewa kason da jihar Kuros Riba ke samu daga gwamnatin tarayya bai kai kuɗin albashin ma'aikata ba, The Cable ta rahoto.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Farfesa Ayade ya ce duba da abinda jihar ke samu daga FG ya gaza ƙuɗin albashi kaɗai, ya cancanci mutanen Kuros Riba su yaba masa bisa kokarin da ya yi na cike giɓin.

A kalamansa, Ayade ya ce:

"Bari na faɗa muku, jihar Kuros Riba ce ta ɗaya a Najeriya idan ana zancen biyan kuɗin Albashi da haƙƙoƙin 'yan fansho amma mu ne na karshe 36 a ɓangaren samun kuɗin shiga daga FG."
"Biyan albashi da fansho hakkokin jama'a ne ba nasara ba, amma a yanzu kam ya dace mu kira hakan babbar nasara saboda giɓin tsakanin abinda muke samu da albashin da muke biya ya nuna tazara mai girma."

Kara karanta wannan

Bautar Ƙasa: Bai Kamata Shirin NYSC Ya Zama Wajibi Ba, Farfesa Jega

"Idan yau ka shigo Kuros Riba, ni tauraron jarumi ne. A taƙaice, na kan taya kaina murna, haka nan mazauna jihar Kuros Ribas na taya ni murna."

Osinbajo Ya Kamata APC Ta Tsayar Takara a Zaben 2023, Peter Obi

A wani labarin kuma Peter Obi ya ce ba Tinubu ya kamata jam'iyyar APC mai mulki ta baiwa tikitin takarar shugaban ƙasa ba da ace tana son ci gaban Najeriya.

Tsohon gwamnan jihar Anambra ya ce sai da ya gaya wa APC cewa idan har suna kaunar Najeriya ta koma kan ganiyarta to su baiwa Osinbajo takara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262