Kada a Haura Shekaru 70, Kuma Wa’adi 3: Gwamna Ya Ba da Shawarin Sanya Wa’adi Ga ’Yan Majalisu da Sanatoci
- Gwamnan jihar Ebonyi ya ba da shawarar yadda za a kawo sauyi a majalisar tarayya ta 10 a kasar
- Umahi ya ce ya kamata a sanya dokar kada kowane dan majalisa ya wuce shekaru 70 a duniya a Najeriya
- Sannan ya ce dole a duba tsarin takara da ake yi, inda yace kada dan takara ya wuce wa'adi uku a kujera
Jihar Ebonyi - Gwamnan jihar Ebonyi kuma zababben sanata a majalisar dattawa, Dave Umahi ya ba da shawarin yadda ya kamata tsarin majalisar tarayya ya kasance.
Gwamnan ya ce bai kamata dan majalisa ya wuce shekaru 70 ba a duniya, sannan bai kamata ko wane dan majalisa ya wuce wa'adi uku ba.
Gwamna Umahi ya yi wannan bayani ne a hirarsa da gidan talabijin na Channels a ranar Laraba 17 ga watan Mayu a Abuja.
A cewarsa:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“Ina ba da shawari duk wani dan majalisa a kayyade masa yawan takara, kuma ya kamata a kayyade yawan adadin shekarun ‘yan majalisa.
“Hakan ya na da muhimmanci, za a iya ba su yawan wa'adin da bai wuce uku ba, shekarunsu kuma kada ya wuce 70 a duniya, hakan zai fi kyau.”
Umahi ya yi kaca-kaca da gwamnonin da basu cancanta ba
Da yake maida martani, Umahi ya soki masu cewa gwamnonin da aka zaba zuwa majalisar basu da kwarewa don zama ‘yan majalisu.
Umahi ya kara da cewa:
“Majalisa ba wurin yin ritaya ta gwamnoni ba ce, wuri ne da suke son ba da tasu gudumawa musamman irin kwarewar da suka samu lokacin da suke mulkin jihohinsu daban-daban don kawo ci gaban kasa baki daya."
Yanzu dai Umahi zai shiga majalisa
An zabi Umahi a matsayin dan majalisa mai wakiltar Ebonyi ta Kudu a majalisa ta 10 wadda za a kaddamar a watan Yuni mai zuwa, ya nemi takarar shugabancin majalisar kafin jam’iyya mai mulki ta tura shugabancin zuwa Kudu maso Kudu.
Rahotanni sun bayyana cewa, gwamnan ya yi alkawarin bin umarnin jam’iyyar akan shugabancin majalisar saboda yana mutunta zababben shugaban kasa, Bola Tinubu.
Ya kara da cewa a yanzu haka yana daya daga cikin masu goyon bayan tsohon gwamnan Akwa Ibom don ganin ya zama shugaban majalisar dattawa ta 10.
Kalu, Umahi ko Akpabio: Ganduje Ya Fadi Wanda Zai Zama Shugaban Majalisar Dattawa
A wani labarin, gwamnan Kano Umar Ganduje ya yi karin haske akan wanda zai kasance shugaban majalisar dattawa.
Ganduje ya ce ana sa ran tsohon gwamnan Akwa Ibom, Godswill Akpabio ne zai kasance a wannan matsayi ta majalisa ta 10.
Asali: Legit.ng