Da Dumi-Dumi: Kotu Ta Sake Dage Karar Peter Obi Kan Nasarar Bola Tinubu
- Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa ta ɗage sauraron ƙarar da Peter Obi ya shigar kan zaɓen shugaban ƙasa
- Kotun ta ɗage sauraron ƙarar ne hr zuwa ranar Juma'a, 19 ga watan Mayu domin ɗorawa daga inda aka tsaya a sauraron ƙarar
- Alƙalin kotun ya ɗage sauraron ƙarar ne saboda ɓangarorin sun kasa cimma matsaya kan wasu takardu da ake buƙata a ƙarar
Abuja - Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa, mai zamanta a birnin tarayya Abuja, ta sake ɗage zaman fara sauraron ƙarar da Peter Obi ya shigar kan nasarar Bola Tinubu.
Jaridar Vanguard ta kawo rahoto cewa, kotun ta ɗage sauraron ƙarar ne har zuwa ranar Juma'a, 19 ga watan Mayun 2023.
Peter Obi, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour Party (LP), yana ƙalubalantar nasarar da zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya samu a zaɓen shugaban ƙasa na ranar 25 ga watan Fabrairun 2023.
Rigima Sabuwa: Shugaban Tsagin Jam'iyyar Labour Party Ya Sha Da Kyar a Kotun Zabe, Bidiyon Ya Bayyana
Peter Obi ya halarci cigaba da zaman fara sauraron ƙarar na yau Laraba, 17 ga watan Mayun 2023.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kotun wacce mai shari'a Haruna Tsammani ya ke jagoranta, ta ɗage sauraron ƙarar ne, saboda ɓangarorin biyu sun kasa cimma matsaya akan wasu takardu da kuma wasu dalilan daban.
A zaman kotun na ranar Laraba, lauyan jam'iyyar Labour Party da Peter Obi, Livy Uzoukwu, SAN, ya gayawa kotun cewa hukumar INEC ta ƙi ba su kaso 70 na takardun da suke buƙata domin cigaba da ƙarar.
Ya yi bayanin cewa hukumar ta ƙi yarda ta ba su iznin duba takardun da suka shafi jihohin Rivers da Sokoto dangane da fom ɗin EC8A.
Da ya ke gabatar da martaninsa, lauyan INEC, A.B Mahmoud, ya ce ya yi mamakin abinda Uzoukwu ya gayawa kotun.
Ya ce a lokuta da dama ya yi ƙoƙarin ganin sun samu zama a tsakaninsu amma abin ya faskara, inda ya ƙara da cewa lokaci na ƙarshe da suka yarda su zauna, lauyoyin LP ficewa suka yi daga wajen zaman na su.
Shugaban Tsagin Jam'iyyar Labour Party Ya Sha Da Kyar a Kotun Zabe
A wani labarin na daban kuma, shugaban tsagin jam'iyyar Labour Party, Lamidi Apapa, ya sha da kyar a hannun magoya bayan jam'iyyar, a kotun zaɓen.
Wasu magoya bayan jam'iyyar ne dai suka yi masa ƙawayan lokacin da ya ke fitowa daga cikin kotun, inda sai da jami'an tsaro suka shiga tsakani.
Asali: Legit.ng