Gwamnatin Buhari Samar da Sabbin Ayyuka Miliyan 12m a Najeriya, Garba Shehu
- Gwamnatin shugaba Buhari ta samar wa yan Najeriya miliyan 12m sabbin ayyuka a ɓangaren noma kaɗai
- Babban mai taimakawa shugaban kasa kan harkokin yaɗa labarai da midiya, Malam Garba Shehu, ne ya faɗi haka
- Ya ce Buhari ya baiwa maraɗa kunya a bangaren noma, wutar lantarki, yaki da cin hanci da rashawa da sauransu
Abuja - Kakakin shugaban ƙasa, Malam Garba Shehu, ya yi ikirarin cewa gwamnatin shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ta samar da sabbin ayyuka miliyan 12m a ɓangaren noma kaɗai.
Shehu ya yi wannan furucin ne yayin hira da Channels tv a shirinsu mai suna 'Sunrise Daily'. Ya ce gwamnati mai ci ta tabuka abin a zo a gani a bangarori da dama.
A cewarsa, gwamnatin shugaba Buhari, wacce wa'adinta ke gab da karewa, ta yi abinda ake tsammani a ɓangaren tsaro, samar da wutar lantarki, yaƙi da cin hanci da sauransu.
Daily Trust ta rahoto Shehu ya ce:
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
"A bangaren noma kaɗai, ƙungiyar manoman shinkafa a Najeriya (RIFAN) tana maganar samarwa mutane miliyan 12m sabbin ayyuka, ka duba wannan abu a ɓangaren aikin gona kaɗai."
"Kamfanonin taki huɗu kacal wannan gwamnatin ta gada, amma yanzu akwai kamfanin yin taki 52 kuma duk suna aiki. Shiyasa sabbin manoman shinkafa miliyan N12m ba su da matsalar takin gona."
"A yau mun wayi gari Manoman mu ke noma Shinkafar da muke ci. Najeriya ta samu wadatar abinci, ta kirkiro hanyoyi daban-daban na gina tattalin arziki, mun daina dogaro da mai."
Yanzu FG ta daina shigo da Shinkafa yar waje- Shehu
Malam Garba Shehu ya ƙara da cewa a baya Najeriya na kashe dala biliyan $5bn kowace rana wajen shigo da Shinkafar waje, amma zuwan wannan gwamnatin, ko sisi ba'a fitarwa yanzu.
Gwamnan Jihar Taraba Ya Bayyana Gaskiya Dangane Da Batun Fitar Da N2bn a Asusun Jihar Domin Siyo Motocin Kece Raini
"Kafin zuwan gwamnatin Buhari, ƙasar nan tana kashe dala biliyan $5bn kowace rana domin shigo da Shinkafa, amma a yau ko dala ɗaya bata fita daga CBN da nufin shigo da Shinkafar waje."
Osinbajo Ya Amince a Kafa Sababbin Jami’o’i 36 a Najeriya
A wani labarin kuma Majalisar zartaswa ta amince da kafa sabbin jami'o'i 36 a faɗin Najeriya duk da shugaban kasa ba ya nan
Ministan ilimi, Adamu Adamu, ya ce taron FEC wanda ya samu jagorancin mataimakin shugaban ƙasa, ya aminta yan kasuwa masu zaman kansu su kafa makarantun.
Asali: Legit.ng