Tinubu Ya Gana Da Kwankwaso a Paris Kan Batun Shigowarsa Cikin Gwamnatinsa
- Zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Najeriya, Bola Tinubu, ya gana da Rabi'u Musa Kwankwaso, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar NNPP, a birnin Paris
- Tattaunawar wacce ta gudana tsakanin Bola Tinubu da Kwankwaso ta ɗauke su tsawon sa'o'i hudu, kan yiwuwar shigar Kwankwaso cikin gwamnatin Tinubu
- Tinubu ya kuma bayyana buƙatarsa ta ganin ya sulhunta gabar da ke tsakanin Kwankwaso da Ganduje
Paris - Zaɓaɓɓen shugaban ƙasa Bola Tinubu na APC ya yi wani zama da Rabiu Musa Kwankwaso na jam'iyyar NNPP a birnin Paris da ke ƙasar Faransa.
Tattaunawar dai ta gudana ne a ranar Litinin da ta gabata, tsakanin Bola Tinubu da Kwankwaso, wacce ta ɗauke su tsawon sa'o'i hudu.
Tinubu ya ce yana shirin kafa “gwamnatin haɗin kan 'yan ƙasa” wacce za ta haɗa da ‘yan jam’iyyun adawa, dalilin Tinubu da rahotanni suka bayyana na zama da Kwankwason kenan.
“Shugabannin Ƙasa 120 Za Su Halarci Bikin Rantsar Da Tinubu": Cewar Adamu Garba, Jigo a Jam'iyyar APC
Sun tattauna kan batun zaɓen majalissu
Mutanen biyu sun kuma tattauna batun zaɓen shugabannin majalisar dokokin ƙasar da ke tafe. Jam’iyyar APC ta bayyana mutanen da ta ke so su jagoranci tagwayen majalisun.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Sai dai wasu ‘ya’yan jam’iyyar APC na adawa da wannan tsari kuma sun yi barazanar sauya sheƙa zuwa jam’iyyar adawa idan har ba a sauya tsarin ba.
Jam'iyyar NNPP na da Sanatoci biyu da 'yan majalisar wakilai 19. Idan har waɗannan ‘ya’yan jam’iyyar za su haɗa ƙarfi da ƙarfe da ‘yan adawa, za su iya hana jam’iyyar APC samun rinjaye a yayin zaɓen.
Wadanda suka halarci ganawar baya ga Kwankwaso
Ganawar tsakanin Tinubu da Kwankwaso ta samu halartar Femi Gbajabiamila, kakakin majalisar wakilai kuma shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa mai jiran gado.
Abdulmumin Jibrin, dan majalisar wakilai na NNPP kuma tsohon jigo a kungiyar yaƙin neman zaɓen Tinubu, shi ma ya samu halarta.
Oluremi Tinubu, uwargidan shugaban ƙasa, ta karbi Salamatu Kwankwaso, matar Rabiu Musa Kwankwaso.
Rahotanni sun bayyana cewa mutanen biyu sun tuno da irin dangantakarsu da ta samo asali tun a shekarar 1992. A wancan lokacin Tinubu ya kasance Sanata ne, Kwankwaso kuma shi ne mataimakin kakakin majalisar wakilai.
Kwankwaso ya ce zai yi shawara da mutanensa
The Cable ta ce Kwankwaso ya ce zai tattauna da masu ruwa da tsaki a bangarorin biyu domin jin ta bakinsu kafin ya amince.
Ana sa ran Tinubu zai yi wa Kashim Shettima, da kungiyar gwamnonin APC, da sauran shugabannin jam’iyyar bayani, a yayin da shi ma Kwankwason zai yi haka ga shugabancin jam’iyyarsa.
Tinubu ya nuna damuwarsa kan alaƙar Kwankwaso da Ganduje
Tinubu ya kuma bayyana damuwarsa kan yadda dangantaka ta yi tsami tsakanin Abdullahi Ganduje, gwamnan jihar Kano mai barin gado da Kwankwaso.
Ganduje ya kasance mataimaki ga Kwankwaso a lokacin yana gwamnan Kano daga 2011 zuwa 2015, kafin rabuwarsu.
Yanzu dai jama'a sun zura ido, suna jiran su ga ko Kwankwaso zai aminta da tayin shiga gwamnatin Tinubun ko a'a.
Ina da ƙarfin da zan iya gudanar da mulki
A wani labarin da muka wallafa a baya, kun jiyo Tinubu na bayyana cewa lafiyarsa garas, kuma ya na da ƙarfin da zai gudanar da mulki a jikinsa.
Ya bayyana hakan ne a lokacin da ya dawo daga wata tafiya da ya yi zuwa Faransa.
Asali: Legit.ng