Kotu Ta Tsige Hadimai 18 da Shugabar NDDC Ta Nada Ba Bisa Doka Ba
- Babbar Kotun tarayya ta tunbuke hadimai 18 daga kan mukamansu a hukumar raya yankin Neja Delta (NDCC)
- Yayin yanke hukunci ranar Litinin, Alkalin Kotun ya ce shugabar NDDC, Lauretta Onochie, ta shiga gonar da ba nata ba
- Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da masu sharhi kan ayyukan gwamnati ke yaba wa shugaba Buhari kan yadda ya ɗauko gyaran NDDC
Delta State - Kusan hadimai 18 waɗanda shugabar hukumar raya yankin Neja Delta (NDDC), Lauretta Onochie, ta naɗa sun rasa ayyukansu.
Babbar Kotun tarayya mai zama a Warri, jihar Delta ce ta tsige baki ɗaya hadiman guda 18 daga kan muƙaman da aka naɗa su.
Kotu ta aike da sako da shugabar NDDC
Da yake bayyana hukuncin da Ƙotu ta yanke, Alkalin Kotun, mai shari'a Okon Abanga, ya ce Onochie ta wuce gona da iri, ta shiga aikin da ba nata ba wajen naɗa hadiman.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Haka zalika Kotun ta umarci Onochie ta kakkaɓe hannuntaa kuma karta sake shiga aikin Daraktan gudanarwa na hukumar NDDC, Dakta Samuel Ogbuku, kamar yadda The Nation ta ruwaito.
Kotu ta ɗauki wannan matsaya ne yayin yanke hukuncin a karar da Dakta Mike Oberabor, ya shigar a madadinsa da iyalan Oberabor Oreme-Egbede da ke Olomoro, ƙaramar hukumar Isoko ta kudu a jihar Delta.
Jaridar This Day ta tattaro cewa hukumar NDDC, Onichie da kuma Ogbuku ne waɗanda ake tuhuma na farko, na biyu da na uku a cikin ƙarar.
Buhari ya yi wa NDDC garambawul
Legit.ng Hausa ta rahoto muku cewa wani mai sharhi kan harkokin gwamnati, Nzerem Omehia, ya ce gwamnatin Buhari ta ci 100 bisa 100 a bangaren gyara hukumar NDDC.
A cewarsa, shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya nuna alamun yana da sha'awar raya yankin da ke samar da albarkatun man Fetur a Najeriya.
A wani labarin kuma Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Anambra Ya tsallake Rijiya da Baya a Wani Hadarin Mota
Kakakin majalisar dokokin jihar Anambra, Honorabul Okafor, ya gamu da hatsarin mota, Allah ya masa gyaɗar dogo.
Rahoto ya nuna Honorabul Okapor ya je wurin ne don taimakon wani tsohon Darakta da ya gamu da hatsari, amma sai wata Tirela ta kuskure shi.
Asali: Legit.ng