Batun Rantsuwar Tinubu: Hukumar ‘Yan Sanda Ta Ja Kunnen ‘Yan Siyasa Saboda Kalaman Tunzura Jama'a
- Rundunar 'yan sandan Najeriya ta gargaɗi 'yan siyasar da ke ƙoƙarin kawo ruɗani a ƙasa gami da ƙoƙarin kawo cikas ga bikin rantsar da Bola Tinubu a ranar 29 ga watan Mayu
- Rundunar ‘yan sandan ta ce ta na bin diddiƙin ayyukan waɗannan ‘yan siyasan da kuma sauran duk masu yin zagon ƙasa ga sha’anin tsaro a ƙasar
- Rundunar ta kuma buƙaci ‘yan siyasar da su yi watsi da yunƙurin da suke yi na kawo tashin hankali a ƙasa
Abuja - Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce ta na sanya idanu kan ’yan siyasan da ke ƙoƙarin kawo tsaiko dangane da rantsar da Bola Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima da za a yi a ranar 29 ga watan Mayu.
Babban sufeto janar na ‘yan sandan Najeriya, Usman Baba ne ya bayyana hakan a wata ganawa da manema labarai a hedikwatar rundunar da ke Abuja a ranar Litinin.
Usman Baba ya ce hukumarsu na aikin sanya idanu tare da haɗa gwuiwa da wasu hukumomin tsaro musamman jami’an hukumar leƙen asiri don dakile nufinsa, kamar yadda ya ke a rahoton Daily Trust.
Wasu ‘yan siyasar da suka faɗi zabe ne ke ƙoƙarin kawo hargitsi
Usman Baba ya kuma bayyana cewa, matakin ya zama wajibi ne domin yin maganin mutanen da suka dage kan cewar sai sun kawo cikas ga zaman lafiyar da ake samu a ƙasar nan.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ya ƙara da cewa sun lura da wasu ‘yan siyasar da sakamakon zaben 2023 bai yi wa daɗi ba da yin kalamai na tunzura jama’a, wanda hakan ka iya zama barazana ga bikin rantsar da shugaban ƙasa a ranar 29 ga Mayu da muke ciki.
A kalamansa:
“Rundunar ‘yan sandan Najeriya da haɗin gwiwar jami’an tsaron leken asiri na ƙasa, suna sanya idanu sosai kan ayyukan waɗannan jiga-jigan ‘yan siyasan da ma sauran waɗansu marasa kishin ƙasa, wadanda a koda yaushe suke burin ganin ƙasar ta faɗa cikin hali na tashin hankali da rashin zaman lafiya”
Duk wanda aka kama zai fuskanci fushin hukuma
Ya kuma ƙara da cewa, jami’an tsaro ba za su lamunci irin waɗannan furuci da ka iya jefa ƙasar nan cikin ruɗani ba, inda ya ce duk wani ɗan siyasa da ya yi kunnen uwar shegu da gargaɗin, zai fuskanci fushin hukuma.
Vanguard ta ruwaito Baba ya na cewa za su yi duk mai yiwuwa wajen kare dimukradiyyar kasar nan.
Hakanan kuma Usman Baba ya bayyana cewa duk girman ɗan siyasar da aka samu da irin waɗannan kalamai na tunzuri, to lallai zai fuskanci fushin hukuma.
Tinubu ya naɗa mutane 13 cikin kwamitin rantsar da shugaban kasa
A wani labarin da muka wallafa a kwanakin baya, kun ji cewa Bola Tinubu ya kafa kwamitin mutane 13 na rantsar da shi da za a yi a 29 ga watan Mayun shekarar 2023.
Kwamitin ne zai kula da tsare-tsare da za a yi a yayin gudanar da wannan biki na rantsarwar wanda zai gudana a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya.
Asali: Legit.ng