Majalisa Ta 10: Abbas da Kalu Sun Ziyarci Gwamnan Jihar Legas, Sun Nemi Goyon Bayansa

Majalisa Ta 10: Abbas da Kalu Sun Ziyarci Gwamnan Jihar Legas, Sun Nemi Goyon Bayansa

  • Zaɓin jam'iyyar APC a kujerar shugabancin majalisar wakilai, sun ziyarci gwamnan jihar Legas, Sanwo-Olu
  • Abbas Tajudeen da Benjamin Kalu, sun ziyarci gwamnan ne domin neman haɗin kansa da goyon baya ga takararsu
  • Sun kuma buƙaci gwamnan da ya sanya baki wajen shawo kan sauran ƴan takara su mara mu su baya

Jihar Legas - Zaɓaɓɓen ɗan majalisa kuma mai neman kujerar kakakin majalisar wakilai, Abbas Tajudeen, ya ziyarci gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, domin neman goyon bayan shi.

The Cable ta kawo rahoto cewa, Abbas, wanda shine zaɓin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a kujerar kakakin majalisar, ya gana da Sanwo-Olu ne a Legas ranar Asabar, tare da rakiyar Benjamin Kalu, zaɓin jam'iyyar a mataimakin kakakin majalisar.

Abbas da Kalu sun ziyarci gwamnan jihar Legas
Abbas da gwamna Babajide Sanwo-Olu Hoto: Tajudeen63Abbas
Asali: Twitter

Da ya ke magana a lokacin ziyarar, Abbas ya ce da shi da sauran waɗanda jam'iyyar ta zaɓa, suna buƙatar goyon bayan Sanwo-Olu, domin ya ba sauran ƴan takarar da gwamnoni baki.

Kara karanta wannan

"Dalilin Mu Na Bijirewa Matsayar APC Kan Shugabancin Majalisa Ta 10", Betara Ya Fasa Kwai

Ya ƙara da cewa suna buƙatar shawarar gwamnan domin warkar da raunikan da dambarwar neman shugabancin majalisar ya haifar.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A kalamansa:

"Mun zo nan ne domin kasa mana albarka. Kasancewar ka ɗaya daga cikin gwamnoni masu biyayya ga jam'iyya, mun yi amanna cewa addu'arka da goyon bayan ka, zai taimaka mana sosai wajen cika burikan mu."
"Mu na buƙatar addu'arka domin tabbatar da ba wai kawai nasara za mu yi ba a ranar 13 ga watan Yuni, za mu samu damar daidaita majalisar da yayyafa ruwan sanyi ga duk ƴan takarar da aka ɓata wa rai.
"Mun san cewa kai cikakken ɗan Najeriya ne na gaske, za ka iya tuntuɓar sauran ƴan takarar da gwamnoni, domin tabbatar da mun samu haɗin kai akan wannan ƙudirin na mu."

Da ya ke magana a wajen, Kalu wanda shine kakakin majalisar na yanzu, ya ce shugabancinsu zai tabbatar da daidaito yayin da za su riƙa kallon buƙatun ƴan Najeriya wajen zartar da hukuncinsu, cewar rahoton The Guardian.

Kara karanta wannan

Ta Fasu An Ji: An Fallasa Abinda Tinubu da Gwamna Wike Su Ke Kulla Wa Atiku Abubakar a Kotu

Mai Neman Shugabancin Majalisar Wakilai Ya Bijirewa APC Da Tinubu

A wani rahoton na daban kuma, Idris Waje ya bijirewa matsayar jam'iyyar APC kan shugabancin majalisar wakilai.

Waje ya haƙiƙance cewa yanzu lokacinsa ne na zama kakakin majalisar wakilan, saboda yankinsa bai taɓa da da shugaban majalisar ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng