Betara Ya Bayyana Dalilinsu Na Bijirewa Matsayar APC Kan Shugabancin Majalisa Ta 10

Betara Ya Bayyana Dalilinsu Na Bijirewa Matsayar APC Kan Shugabancin Majalisa Ta 10

  • Ɗaya daga cikin ƴan majalisar da suka yi wa jam'iyyar APC, bore kan kakakin majalisa, ya bayyana dalilan su
  • Mukhtar Aliyu Betara, ya ce sam ba a tuntuɓe su ba kafin jam'iyyar ta bayyana waɗanda ta ke goyon baya su zama shugabannin majalisar
  • Betara wanda shi ma yana daga cikin masu neman kujerar, ya ce dole sai da amincewar su za a samu wanda za a marawa baya

Abuja - Muktar Aliyu Betara, ɗan majalisa mai wakiltar Biu/Bayo/Shani daga jihar Borno, ya bayyana cewa dole abokan takararsa masu neman kujerar kakakin majalisa, a tuntuɓe su kafin a marawa wani baya kan shugabancin majalisa ta 10.

The Cable ta kawo rahoto cewa, da ya ke magana wajen ayyana aniyar Idris Wase, ta zama kakakin majalisa, Betara ya yi tsokaci kan fushin da ƴan majalisar da ke neman kujerar kakakin ke yi, kan matsayar jam'iyyar APC.

Kara karanta wannan

"Yanzu Lokaci Na Ya Yi": Mai Neman Shugabancin Majalisar Wakilai Ya Bijirewa APC Da Tinubu

Betara ya bayyana dalilin su na bijirewa APC
Mukhtar Aliyu Betara, mai neman kakakin majalisar wakilai ta 10 Hoto: Thecable.com
Asali: UGC

Jam'iyyar APC dai ta zaɓi Abbas Tajudeen daga jihar Kaduna a matsayin ɗan takararta a kujerar kakakin majalisa, sannan ta zaɓo Benjamin Kalu daga jihar Abia a matsayin mataimakinsa.

Wannan hukuncin da jam'iyyar ta yanke, bai yi wa masu neman kujerar daɗi ba, inda suka kafa wata ƙungiya domin bijirewa matsayar jam'iyyar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana dalilin su na adawa da matsayar APC

A kalamansa:

"Mu a wajen mu, mun kafa wannan ƙungiyar ne saboda muna adawa da tsarin jam'iyya kan raba muƙamai. Ba faɗa mu ke ba kuma ba zamu yi faɗa ba. Muna goyon bayan a samu ɗan takara ɗaya da kowa ya aminta da shi."
"Za mu iya zaɓar ɗan takarar daga cikin mu, amma idan mu ka zauna mu ka cimma matsaya. Ina tabbatar mu ku da cewa mutum ɗaya kawai Allah zai ba muƙamin kakakin majalisa. Ina ba ku tabbacin ba za mu samu wata matsala ba. Za mu yarda mu marawa ɗaya daga cikin mu baya ya samu kujerar."

Kara karanta wannan

Majalisa Ta 10: Dalili 1 Rak da Yasa Tinubu da APC Suka Zabi Akpabio da Abbas, Shettima Ya Tona Gaskiya

"Mu a wajen mu, wannan ƙungiya da mu ka kafa, ba faɗa mu ke ba, dukkanin mu ƴaƴan APC ne. Za a iya zaɓar ɗan takara ɗaya, amma dole sai mun zaune mun ce ga wanda mu ka zaɓa ya jagorance mu."
Ina tabbatarwa da abokan takara ta, zaɓaɓɓun ƴan majalisa, tsaffin ƴan majalisa cewa, ba zamu yi faɗa ba, za mu yarda mu marawa ɗaya daga cikin mu baya ya zama kakakin majalisa."

Betara shi ma a ranar Litinin, ya ayyana aniyarsa ta neman kakakin majalisar wakilan, cewar rahoton Tribune.

Mai Neman Shugabancin Majalisar Wakilai Ya Bijirewa APC Da Tinubu

A wani rahoton na daban kuma, Idris Wase ya yi fatali da matsayar APC da Tinubu kan kujerar shugabancin kakakin majalisar wakilai ta 10.

Wase wanda shine mataimakin kakakin majalisar na yanzu, ya ce yanzu lokacinsa ya yi da zai ɗare kan shugabancin majalisar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng