Mun Shirya Tafiya Daura: Buhari da Aisha Sun Koma Gidan Shugaban Kasa Mai Barin Gado
- Shugaba Muhammadu Buhari da mai ɗakinsa, Aisha Buhari, sun fara haramar barin fadar shugaban kasa
- Aisha Buhari ta bayyana cewa tuni ita da mijinta suka koma Glass House, gidan da shugaba mai barin gado ke zama
- Mai ɗakin shugaban kasan ta jagoranci matar Tinubu sun zagaye duk inda ya kamata a Aso Rock
Abuja - Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, da uwar gidansa, Hajiya Aisha Buhari, sun fara haramar barin mulki, sun koma "Glass House," gidan shugaban ƙasa mai barin gado da matarsa a cikin Aso Rock.
Rahoton The Cable ya ce Glass House, nan ne gidan da ake warewa shugaban ƙasa da mai ɗakinsa su zauna har zuwa lokacin da zasu bar fadar shugaban ƙasa.
Ana sa ran Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, zababben shugaban ƙasa zai kama aiki ranar 29 ga watan Mayu, 2023 bayan rantsarwa.
Duk da ya koma gidan zababben shugaban kasa 'Depence House' da ke Maitama a Birnin Tarayya Abuja, Tinubu ya fi zama da muƙarrabansa a gidansa da ke Asokoro.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A wani bidiyo da ta wallafa a shafin Instagram ranar Alhamis bayan ta jagoranci uwar gidan shugaban kasa mai jiran gado, Remi Tinubu, sun shiga lungu da saƙo, Aisha ta ce tana fatan za'a kiyaye al'adar miƙa mulki.
Aisha Buhari ta ce:
"Ni da uwar gidan shugaban kasa mai jiran gado, Sanata Remi Tinubu, mun kewaya ko ina na nuna mata asalin gidan. A yanzu mu mun koma Glass House, gidan shugaban kasa mai barin gado."
"Ina ba da shawarin cewa ya kamata Glass House Kamar yadda aka saba ya ci gaba da zama matsugunin shugaban ƙasa mai barin gado. A yanzu da nake magana da ku, ni da Mijina mun koma gidan da zama."
"Mu biyu kaɗai mu ke zaune a nan, ina tunanin haka ya dace a ci gaba kamar yadda aka saba a fadar shugaban kasa."
Ya Zama Dole Na Zama Shugaban Ƙasa a Najeriya, Peter Obi
A wani labarin kuma Ɗan Takarar Shugaban Kasa a Inuwar LP, Peter Obi, Ya ce Ba Makawa Dole Ya Zama Shugaban Najeriya
Tsohon gwamnan jihar Anambra ya faɗi haka ne a wurin taron kaddamar da littafi domin tara kuɗin ɗaukar nauyin karar da Obi ya kalubalanci nasarar Tinubu.
Asali: Legit.ng