Gwamna Masari Ya Kai Ziyarar Bankwana Ga Sarakuna, Ya Nemi A Yafe Masa

Gwamna Masari Ya Kai Ziyarar Bankwana Ga Sarakuna, Ya Nemi A Yafe Masa

  • Gwamna Masari ya yi bankwana da manyan Sarakunan Katsina yayin da ya fara shirin barin Ofis a watan Mayu
  • Yayin ziyarar da ya je fadar sarkin Daura, Masari ya yaba wa Sarakuna bisa goyon bayan da suka baiwa gwamnatinsa
  • Ya kuma roki ɗaukacin Al'umma waɗanda mai yuwuwa ya ɓata musu rai su yafe masa

Katsina - Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina ya kai ziyarar bankwana ga mai martaba Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumin Kabir-Usman, da sarkin Daura, Alhaji Umar Faruq-Umar.

Hukumar dillancin labarai ta ƙasa (NAN) ta tattaro cewa Masari ya ziyarci Masarautar Katsina ranar Laraba, sannan ya wuce Daura ranar Alhamis.

Gwamna Masari.
Gwamna Masari Ya Kai Ziyarar Bankwana Ga Sarakuna, Ya Nemi A Yafe Masa Hoto: Aminu Bello Masari
Asali: Facebook

The Nation ta rahoto cewa wannan ziyarce-ziyarce na bankwana wani ɓangare ne na ƙarewar wa'adin gwamna Masari wanda zai miƙa mulki ranar 29 ga watan Mayu, 2023.

Kara karanta wannan

Tun Yanzu: Kashim Shettima Ta Faɗi Kuskuren da Shugaba Buhari Ya Tafka a Mulkinsa Kamar Na Jonathan

Da yake jawabi a masarautar Daura, Masari ya ce gwamnatinsa ta yi duk mai yuwuwa wajen jawo Sarakuna da Malamai a jiki domin tabbatar da zaman lafiya da haɗin kai a jihar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa, ya kawo ziyarar bankwana ne domin ƙara rokon haɗin kai tsakanin mazauna Katsina, ba tare da la'akari da shiyyoyi, kananan hukumomin ko garuruwa ba.

Ya ce baki ɗaya Katsinawa yan gida ɗaya ne don haka ya yi kira ga ɗaukacin al'umma su ƙara haɗa kansu da zumunta kamar yadda Sardauna, Ahmadu Bello, ya kafa tubali.

Masari ya ce:

"Mun kawo ziyara Masarautu ne domin mu ƙara yaba musu bisa goyon baya da gudummuwar da suka baiwa gwamnatina tsawon shekaru Takwas."

Ya ce gwamnatinsa ta sha fama da kalubale masu illa, musamman abinda ya shafi tsaro, tattalin arziki da kuma annobar korona Birus.

Kara karanta wannan

Ta Fasu An Ji: An Fallasa Abinda Tinubu da Gwamna Wike Su Ke Kulla Wa Atiku Abubakar a Kotu

Masari ya nemi Katsinawa su yafe masa

Daga karshe, gwamna Masari ya roki mutanen da suke ganin gwamnatinsa ta ƙuntata musu ko ta musu ba daidai ba, su yi hakuri su yafe masa.

Gwamna mai barin gado ya ƙara da cewa duk abinda aka ga gwamnatinsa ta yi, da kyakkyawar zuciya ta aikata da nufin kawo ci gaba a jihar Katsina.

A lokacin da Masari ke haramar barin Ofis, wasu Katsinawa sun shaida wa Legit.ng Hausa cewa a halin yanzu sun zura ido su ga abinda sabon gwamna, Dikko Raɗɗa, zai yi.

Wani mai cin gajiyar S-Power da Masari ya kirkiro a mulkinsa, Lawal Adam, ya ce gwamna mai barin gado ya taɓuka bakin gwargwado amma jihar Katsina na bukatar fiye da haka.

A cewarsa yana daga cikin waɗanda suka amfana da gwamnatin Masari domin a lokacinsa ne ya samu ɗan aikin da yake jalauta rayuwar yau da kullum.

Ya ce:

Kara karanta wannan

Majalisa Ta 10: Dalili 1 Rak da Yasa Tinubu da APC Suka Zabi Akpabio da Abbas, Shettima Ya Tona Gaskiya

"Muna yi wa gwamna fatan Alheri, ya kawo tsaruka da suka taimaka kamar S-Power, amma matsalar tsaro ta hana Katsina sakat. Muna jira mu ga abinda sabon gwamna zai mana."

A nasa ra'ayin, Ibrahim Dabai, ba wani muhimmin abu da gwamna Masari ya yi na azo a gani a tsawon mulkinsa na shekara 8, duk da haka ya ce, "Muna masa fatan alheri."

A wani labarin kuma Gwamna Masari ya nada VC na jami'ar UMYUK da shugaban Kwalejin Fasaha Hassan Usman Katsina

Gwamna Aminu Bello Masari ya naɗa sabon VC a jami'ar Umaru Musa Yar'adua (UMYU) da ke jihar Katsina.

Baya ga haka, Gwamna ya naɗa sabon shugaban kwalejin fasaha Hassan Usman Katsina. Ya roki mutane su ba su haɗin kan da ya kamata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262