Abubuwa 20 da za a Rika Tuna Buhari da su Shekaru Bayan Barin Aso Rock - Hadiminsa

Abubuwa 20 da za a Rika Tuna Buhari da su Shekaru Bayan Barin Aso Rock - Hadiminsa

  • Nan da kwanaki 18, Mai girma Muhammadu Buhari zai yi sallama da kujerar shugaban Najeriya
  • Tun Mayun 2015, tsohon sojan ya dare kan mulki a sakamakon nasarar da ya samu a zaben kasar
  • Yayin da yake ban-kwana da fadar Aso Rock, an fara tattaro nasarorin da gwamnatinsa ta samu

Abuja - A shafinsa na Facebook, Buhari Sallau ya jero wasu daga cikin nasarorin mai gidansa, Mai girma shugaban Najeriya mai shirin barin-gado.

Buhari Sallau ya ce za a rika tuna gwamnatin Muhammadu Buhari da abubuwa da-dama, daga cikinsu ya ce akwai gina tituna da hanyoyin jirgi.

Hadimin shugaban kasar ya ce a gwamnatin nan an kawo gyara a bangaren mai da gas, sannan an saukaka kasuwanci baya ga inganta aikin gona.

Buhari
Muhammadu Buhari a Aso Rock Hoto: @BashirAhmaad
Asali: Facebook

Shi ma Bashir Ahmaad ya jero wadannan ayyuka a shafinsa na Twitter a ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Abin da Ya Sa Ake Bada Kwangilolin Biliyoyi a Karshen Mulkinmu – Gwamnatin Buhari

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Amma wasu masu tofa albarkacin bakinsu a kafafen sada zumunta sun nuna su na da ja, a cewarsu ba a samu nasarorin a buga-a jarida a bangarorin ba.

Kokari 20 da gwamnatin Buhari tayi

1. Gyaran dokokin majalisa

2. Cikakkun dokoki masu iko

3. Abubuwan more rayuwa: Jirgin kasa, tituna, tashohin jirgin sama da ruwa, lantarki, gidaje, ruwa

4. Dokokin saukaka kasuwanci

5. Tattalin arzikin zamani da shaidar zama ‘dan kasa

6. Gyara harkar fetur da gas

7. Albarkatun ma’adanai

8. Sauya harkar noma

9. Inganta rayuwar marasa karfi da yaki da talauci

10. Sha’anin ilmi da kiwon lafiya

11. Yara harkar kasuwanci, tattallin arziki da darajar kudi

12. Taimakawa Jihohi

13. Wasanni da harkar fasaha

14. Cigaban Neja Delta

15. Yaki da rashin gaskiya

16. Tabbatar da bin doka, harkar tsaro da gyara shari’a

17. Alakar kasa da kasa

18. Huldatayyar kasashen waje

19. ‘Yan Najeriya sun samu makamai a Duniya

20. Yakar annobar COVID-19

Kara karanta wannan

Bola Tinubu Ya Bar Najeriya Zuwa Ƙasar Turai, An Bayyana Abu 2 da Zai Maida Hankali

Fursunoni sun koshi

A rahotonmu, an ji yadda Gwamnatin Tarayya ta ware Naira biliyan 22 domin a ciyar da fursunonin da ke tsare a gidajen gyaran halin da ke kasar nan.

Babban sakatare a Ma'aikatar harkokin cikin gida, Dr. Shuaib Belgore ne ya bayyana haka, ya kuma nuna bukatar sake gina wasu sababbin gidajen yari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng