Har Yanzu Tinubu Bai da ‘Dan Takara a Zaben Shugabannin Majalisa – Zababben Sanata

Har Yanzu Tinubu Bai da ‘Dan Takara a Zaben Shugabannin Majalisa – Zababben Sanata

  • Joel-Onowakpo Thomas ya ce har zuwa yanzu bai tsaida wanda zai goyi baya a zaben Majalisa ba
  • Zababben Sanatan ya kuma yi ikirarin Bola Tinubu bai tsaida ‘dan majalisar da yake goyon baya ba
  • Hon. Joel-Onowakpo ya nuna ba za su yarda zababben shugaban kasa ya yi masu karambani ba

Delta - Sanatan da zai wakilci Kudancin jihar Delta a majalisa ta goma, Joel-Onowakpo Thomas ya ce Bola Tinubu bai ayyana ‘dan takara ba.

A rahoton This Day, an ji Honarabul Joel-Onowakpo Thomas yana mai cewa a iyakar saninsa, Bola Tinubu bai goyo bayan wani a zaben majalisar bana.

Joel-Onowakpo ya fadawa ‘yan jarida cewa duk wanda zai jagorance su zai kasance ya samu goyon bayan akasarin ‘yan majalisar dattawan kasar.

Zababben Sanatan PDP
Joel-Onowakpo Thomas Hoto: tribuneonlineng.com
Asali: UGC

Da ya zanta da manema labarai a garin Warri, ‘dan siyasar ya yi magana a kan yadda ya fara shiga siyasa har ya kai matsayin da ake alfahari da shi a yau.

Kara karanta wannan

Abin da ‘Yan Takaran Kujerun Majalisa Su ka Fadawa Shugaban Jam’iyyar APC Gar da Gar

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Rahoton ya ce Joel-Onowakpo ya yi magana a kan zaben Sanata da ya shiga da abin da ake sa ran zai yi wa mutanen Kudancin Delta a majalisar dattawa.

A game da zaben shugabanni da za ayi, Joel-Onowakpo ya ce bai da masaniyar an ayyana wani ‘dan takara, ya ce a iyaka saninsa, jita-jita ce ke yawo.

'Yan majalisa su na da 'yanci

Da yake jawabi a ranar Laraba, zababben Sanatan ya roki ‘yan jarida su yi hattara da irin rahotonsu, ya ce ka da su jefa zababben shugaban kasa a matsala.

Zababben Sanatan ya tabbatar da cewa ba za su zama ‘yan amshin-shatan Gwamnatin Bola Tinubu ba, Tribune ta fitar da wannan rahoto dazu.

Sanatan mai jiran gado ya ce sha’anin shugabancin majalisa yana da muhimmanci.

Kwararren Akantan ya ce hakkin abokan aikinsa ne su zabi wanda suke so ya zama shugaban kasa, babu dalilin ayi masu katsalandan daga waje.

Kara karanta wannan

Ba a Haka: Inda Tinubu Ya Yi Kuskure Wajen Shugabancin Majalisar Dattawa – Sanata

Idan aka tambaye ni, zan ce Ahmed Tinubu bai ayyana kowa ba, a iyakar abin da na sani. Kofa a bude ta ke, duk mai sha’awa zai iya neman takara.

Ko da shi ma bai da 'dan takara, amma ya ce idan Tinubu ya tsoma baki, ya yi shisshigi.

Sai 29 ga Mayu za mu tafi

A jiya ne aka ji labari Ministan sufuri, Muazu Sambo ya ce an zabi wannan gwamnati domin tayi aiki ne daga 2019 zuwa 29 ga watan Mayun 2023.

Ministan ruwa, Sulaiman Adamu ya ce haka zalika su na sa ran gwamnati mai zuwa za tayi aiki har ranar karshenta a ofis watau 29 ga Mayun 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng