Abin da Ya Sa Ake Bada Kwangilolin Biliyoyi a Karshen Mulkinmu – Gwamnatin Buhari
- Kwanakin kadan suka rage wani sabon Shugaban kasa ya gaji Muhammadu Buhari a karagar mulki
- Amma har gobe Gwamnatin tarayya ta na cigaba da amincewa da bada wasu kwangiloli a Najeriya
- Ministocin da ke rike da ma’aikatar sufuri da wutar lantarki sun fadi hikimar cigaba da aikin FEC
Abuja - Gwamnatin tarayya ta dauki lokaci wajen yi wa al’umma bayanin abin da ya sa majalisar zartarwa watau FEC ta ke amincewa da kwangiloli.
Yayin da gwamnatin Muhammadu Buhari ta zo karshe, sai aka ji FEC ta yi na’am da wasu kwangilolin biliyoyin kudi, Daily Trust ta kawo dalilin haka.
Ministan sufuri na tarayya, Mu’azu Sambo da takwaransa na ma’aikatar harkar ruwa, Sulaiman Adamu sun yi wa 'yan jarida karin haske a jiya.
Sai 29 ga Mayu za a canza gwamnati
Injiniya Mu’azu Sambo yake cewa bada wani sabon aiki bai nufin gwamnatinsu za ta zarce 29 ga watan Mayu kafin ta mika mulki ga sabon shugaba.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Mai girma Ministan ya ce za su cigaba da aikinsu har zuwa ranar karshe, 28 ga Mayun 2023.
"An zabi wannan gwamnati domin tayi aiki ne daga 2019 zuwa 29 ga watan Mayun 2023, yanzu saboda saura wata daya a mika mulki, sai mu daina aiki?
Dole gwamnati tayi aiki. Mu na sa ran gwamnati mai zuwa za tayi aiki har ranar karshenta a ofis.
- Muazu Sambo
Haka zalika an rahoto Sulaiman Adamu yana cewa gwamnatin da za ta gaji Mai girma Muhammadu Buhari, za ta daura ne daga inda ya tsaya.
Adamu ya ce akwai matakan da ake bi wajen tafiyar da gwamnati, har yanzu ana amfani ne da kasafin kudin 2022, abin ya fi karfin aiki rana guda.
Yadda gwamnati ta ke aiki - Minista
"Akwai takardu da-dama da aka kai gaban BPP da ICRC, dole duk hukumomin da ke aikin su shirya.
A dalilin haka a duk lokacin da suka shirya, wannan ne lokacin da za mu mika takarda. Kamar yadda Ministan sufuri ya fada, mu na ofis har 28 ga Mayu.
- Sulaiman Adamu
Ministan ya ce umarnin da suka samu kenan daga wanda ya nada su, Muhammadu Buhari.
Rikicin jihar Kano
Rahoto ya nuna ‘Yan jam’iyyar NNPP sun ce a kan kudin da ba su kai N10m ba, aka yi gwanjon ma’aikata guda ga wani 'Dan Gwamna Abdullahi Ganduje.
Dr. Abdullahi Baffa Bichi ya ce idan aka rantsar da Abba Kabir Yusuf, za a fahimci barnar da aka yi a Kano daga 2015 a karkashin mulkin APC a jihar.
Asali: Legit.ng