An Shiga Jimami Da Zubar Hawaye Yayin Da Tsageru Suka Kashe Aminin Tinubu a Imo
- ‘Yan bindiga sun hallaka wani jigo a jam’iyya mai mulki ta APC a jihar Imo Kyaftin Tony Enock
- Marigayin an kashe shi ne akan hanyarsa ta zuwa taron masu ruwa da tsari na jam’iyyar kusa da Kwalejin Fasaha ta Awomama
- Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Henry Okoye ya ce ba su samu rahoton wannan lamari da ya faru ba amma zasu yi bincike
Jihar Imo – Rahotannin da ke samunmu yanzu sun tabbatar da mutuwar Kyaftin Tony Enoch wanda jigo ne a jam’iyya mai mulki ta APC.
Jaridar Legit ta tattaro cewa wasu ‘yan bindigan da ba a san ko su waye ba ne suka harbe Kyaftin Enoch lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar.
Taron kamar yadda rahotanni suka tabbatar ya gudana ne a cikin karamar hukumar Oru ta gabas dake jihar Imo.
‘Yan bindigan sun kashe shi ne a kusa da Kwalegin Fasaha ta Awomama dake cikin karamar hukumar, inda aka tsinci gawarsa a bayan motarsa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Wasu majiyoyi da suka tabbatar da aukuwar lamarin a idonsu sun ce ‘yan bindigan sun yi wa marigayin ne kwanton bauna, suka sa ya tsaida motarsa sannan suka harbeshi sau biyu a kayi.
'Yan sanda basu samu labari ba
Jaridar Sahara Reporters ta ce kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Henry Okoye yace ba shi da masaniyar faruwar wannan lamarin.
Ya kara da cewa za su zurfafa bincike don su tabbatarwa kafin daga bisani su fidda sanarwar abin da ya faru, daga nan kuma sai su dukufa wurin bincike da zakulo wadanda suka aikata wannan aika-aika.
Kafin rasuwarshi, marigayin wanda tsohon soja ne ya na da alaka mai karfi kuma ta kusa da gwamnan jihar, Hope Uzodinma wadanda dukkansu kuma suka fito daga karamar hukuma daya.
Gwamnan Uzodinma na Imo Ya Ce Ba Zai Iya Bada Tsaro a Jihar Ba
A wani labarin, Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo ya tabbatar da cewa ba zai iya ba da tsaro a jihar ba muddin aka bar masa shi kadai.
Gwamnan ya yi wannan bayani ne lokacin ganawarsa da shugaba Muhammadu Buhari a Abuja, inda ya zanta da 'yan jaridu ya kuma ce dole a hada karfi da karfe don kawo karshen rashin tsaro a jiharsa dama kasar gaba daya
Asali: Legit.ng