Ba zan iya bada tabbacin tsaro a jihar Imo ba, inji Gwamna Uzodimma

Ba zan iya bada tabbacin tsaro a jihar Imo ba, inji Gwamna Uzodimma

- Lallai ne masu ruwa da tsaki, shugabannin siyasa da gargajiya da na addini su shiga tsakani, a cewar gwamnan.

- Duk da cewa ya yarda lamura ba sa tafiya daidai a jihar, ya gargadi masu tayar da kayar baya

- Amma hukumomi a jihar suna iya bakin kokarinsu

Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodinma, ya bayyana cewa ba zai iya tabbatar da tsaro a jihar ba idan aka bar komi a hannunshi shi kadai.

Bayan ganawa da Shugaba Muhammadu Buhari ranar Talata a fadar Shugaban Kasa da ke Abuja, Uzodimma ya shaida wa manema labarai cewa masu ruwa da tsaki, ciki har da shugabannin gargajiya da na addini da na siyasa, dole ne su kara tattaunawa tare domin wanzar da zaman lafiya a jihar.

A cewarsa, tsoffin masu rike da mukaman siyasa, wadanda suka kasa yin magana a kan ayyukan masu tayar da zaune tsaye, suna da tambayoyin da ya kamata su amsa.

"Idan suka yi magana game da ayyukan ashsha na wadanda ke kawo hargitsi a kasar a da, abin ya sha bamban yanzu," inji shi.

KU DUBA: Gwamnatin Najeriya na shawarar yanke hukuncin kisa ga duk wanda aka kama da lalata layin dogo

Ba zan bada tabbacin tsaro a jihar Imo ba, inji Gwamna Uzodimma
Ba zan bada tabbacin tsaro a jihar Imo ba, inji Gwamna Uzodimma
Asali: Facebook

KU KARANTA: Masu neman raba kasar nan shaidanu ne, Mai Alfarma Sarkin Musulmi

Ya kara da cewa ya je fadar Shugaban Kasar ne domin yi wa Shugaban Kasar bayani game da halin da jihar ke ciki.

Duk da yake ya yarda cewa lamura ba sa tafiya daidai a kasar, Gwamnan ya yi gargadin cewa wadanda ke barnata dukiyar gwamnati lallai ne su shirya girbar abin da suka shuka.

“Duk da cewa rashin tsaro ya zama ruwan dare a duk fadin Najeriya, amma hukumomi a Imo suna iya bakin kokarinsu domin shawo kan lamarin.

“Ya zuwa yanzu, yanayi ya fara daidaita a Jihar Imo idan aka kwatanta da yadda yake a baya. Mutane na iya zuwa su yi kasuwanci. Rayuwar yau da kullun ta dawo a cikin jihar. Hukumomin tsaro sun shawo kan lamarin da ake ciki,” inji shi.

Gwamnan ya yi watsi da zargin cewa kalamansa na baya-baya inda yake kawar da batun tattaunawa na daga cikin abin da ya kara rura wutar halin da ake ciki a jihar.

“Wannan shi ne tunaninsu. Ban san irin furucin da na yi ba wanda ke nuna cewa na rufe kofar sulhu. Ban rufe kofa ba,” Inji Gwamnan.

A jihar Kaduna kuwa, an samu rudani a Birnin Yero da ke kan hanyar Kaduna zuwa Zaria lokacin da wasu 'yan bindiga suka sace wasu matan gida uku a cikin garin.

An tattaro daga majiyoyin yankin da ke cewa an yi garkuwa da mutane 10 lokacin da wasu dauke da makamai suka afka wa yankin da misalin karfe 11 na daren Litinin.

Wani mazaunin garin, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya shaida wa Daily Trust cewa daga cikin wadanda lamarin ya rutsa da su har da ‘ya’yan shugaban yankin guda biyu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel