Kotu Ta Dage Sauraron Karar Atiku Abubakar Kan Zaben Shugaban Kasa, Ta Sanya Sabon Lokaci

Kotu Ta Dage Sauraron Karar Atiku Abubakar Kan Zaben Shugaban Kasa, Ta Sanya Sabon Lokaci

  • Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ta ɗage sauraron karar da Atiku Abubakar da jam'iyyar PDP, suka shigar a gabanta
  • Kotun ta ɗage sauraron ƙarar har zuwa ranar 18, ga watan Mayu, domin ɗorawa daga inda ta tsaya dangane ƙarar zaɓen shugaban ƙasa
  • Atiku Abubakar ya dai garzaya kotun ne inda ya ke neman ta ƙwace satifiket ɗin cin zaɓe da hukumar INEC, ta ba ɗan takarar jam'iyyar APC, Bola Tinubu

Abuja - Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa, mai zamanta a birnin tarayya Abuja, a ranar Alhamis ta ɗage ɗage cigaba da sauraron ƙarar da jam'iyyar PDP da ɗan takararta Atiku Abubakar, suka shigar suna ƙalubalantar sakamakon zaɓen shugaban ƙasa.

Jaridar Vanguard ta kawo rahoto cewa, kotun mai alƙalai biyar wacce mai shari'a Haruna Tsammani, ke jagoranta, ta ɗage sauraron ƙarar har sai zuwa ranar 18 ga watan Mayu, domin cigaba da zaman fara sauraron ƙarar.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Atiku Ya Dira Da Tawagarsa Wajen Sauraron Karar Zaben Shugaban Kasa

Kotu ta dage sauraron karar Atiku Abubakar kan zaben shugaban kasa
Atiku Abubakar tare da 'yan tawagarsa a zaman kotun Hoto: DailyTrust.com
Asali: UGC

Lauyan masu shigar da ƙara, Cif Chris Uche, (SAN) ya gayawa kotun cewa sun zauna da sauran lauyoyin jam'iyyun, inda suka amince kan hanyoyin da za a bi domin tabbatar an kammala fara zaman sauraron ƙarar cikin nasara, cewar Gazettengr.

"Mai girma mai shari'a, lauyoyin jam'iyyun mun zaune tare, inda muka haɗa hannu wajen duba muhimman batutuwan da suka shafi fara zaman sauraron ƙarar." A cewarsa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A yayin da ya ke ɗage zaman sauraron ƙarar, mai shari'a Tsammani, ya yabawa ɓangarorin bisa haɗin kansu da matsayar da suka cimma, inda ya ce hakan zai taimaka wajen kammala zaman fara sauraron ƙarar, ba tare da wani ɓata lokaci ba.

Atiku Abubakar, a cikin ƙarar da ya shigar tare da jam'iyyar PDP, mai lamba CA/PEPC/05/2023, yana neman a kwace satifiket ɗin cin zaɓen da hukumar INEC ta ba Bola Tinubu, na jam'iyyar APC.

Kara karanta wannan

Kafin Ya Shilla Turai, Tinubu Ya Yi Kus-Kus Da Zabin APC a Shugabancin Majalisar Wakilai, Bayanai Sun Bayyana

Atiku Ya Dira Wajen Sauraron Karar Zaben Shugaban Kasa

Da zu rahoto ya zo cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya isa wajen sauraron ƙarar zaɓen shugaban ƙasa.

Atiku ya isa kotun ne dai tare da tawagarsa wacce ta ƙunshi manyan jiga-jigan jam'iyyar PDP.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng