Da Dumi-Dumi: Atiku Ya Dira Wajen Sauraron Karar Zaben Shugaban Kasa
Abuja - Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya isa harabar kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa.
Ɗan takarar na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), a zaɓen shugaban ƙasa na ranar 25 ga watan Fabrairu, ya samu rakiyar wasu manyan jiga-jigan jam'iyyar, cewar rahoton Daily Trust.
Tsohon gwamnan jihar Cross River, Liyel Imoke da Boni Haruna, tsohon gwamnan jihar Adamawa, na daga cikin waɗanda suka raka Atiku a wajen sauraron ƙarar, rahoton Vanguard ya tabbatar.
Shugaban jam'iyyar PDP na ƙasa, Umar Iliya Damagun, da Dino Melaye, ɗan takarar jam'iyyar a zaɓen gwamnan jihar Kogi na watan Nuwamba mai zuwa, sun samu halartar zaman kotun.
A ƙarshen zaman kotun na ranar Laraba, an ɗage cigaba da fara sauraron ƙarar har sai zuwa ranar Alhamis, da misalin ƙarfe 2 na rana.
Kafin Ya Shilla Turai, Tinubu Ya Yi Kus-Kus Da Zabin APC a Shugabancin Majalisar Wakilai, Bayanai Sun Bayyana
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Sai dai zaman kotun ya fara kafin lokacin da aka tsara za a fara gudanar da shi.
Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour Party (LP), Peter Obi, ya halarci fara zaman kotun a ranar Litinin.
Atiku Abubakar da Peter Obi, na ƙalubalantar nasarar da zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya samu a zaɓen shugaban ƙasa.
Asali: Legit.ng