Kafin Ya Shilla Turai, Tinubu Ya Yi Kus-Kus Da Zabin APC a Shugabancin Majalisar Wakilai, Bayanai Sun Bayyana
- Zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya gana da ƴan takarar da jam'iyyar APC ke goyon baya a shugabancin majalisar wakilai
- Bola Tinubu dai ya sanya labule ne da Abbas Tajudeen da Benjamin Kalu, tare da wasu zaɓaɓɓun ƴan majalisar wakilai
- Bayan kammala taron, shugaban ƙasar mai jiran gado ya shilla nahiyar Turai, domin gudanar da wata ziyarar aiki
Abuja - Zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, a ranar Laraba, ya sanya labule da ƴan takarar da jam'iyyar All Progressives Congress (APC), ke marawa baya, a kujerar kakakin majalisa da ta mataimakinsa majalisa ta 10.
Jaridar The Punch, tace Tinubu, ya gana da Hon. Tajudeen Abbas da Hon. Benjamin Kalu, waɗanda jam'iyyar APC ta zaɓa a matsayin ƴan takararta a shugabancin makalisar wakilan, jim kaɗan kafin ya shilla zuwa nahiyar Turai.
A wata sanarwa da mai magana da yawun Tinubu, Tunde Rahman ya fitar, ya bayyana cewa wata tawaga ce ta musamman ta gabatar da Abbas da Kalu a gaban Tinubu, a masaukinsa da ke a Defence House.
Tinubu, wanda jim kaɗan bayan taron ya fice daga ƙasar nan zuwa nahiyar Turai, domin ziyarar aiki, ana sa ran zai kammala tsara shirye-shiryen karɓar mulki a lokacin ziyarar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A ranar Litinin ne dai, jam'iyyar APC ta sanar da tsohon ministan harkokin yankin Niger Delta, Godswill Akpabio, a matsayin ɗan takararta a shugabancin majalisar dattawa ta 10.
Jam'iyyar ta kuma amince da Sanata Barau Jibrin, a matsayin mataimakin shugaban majalisar dattawan na gaba.
A majalisar wakilai kuwa, jam'iyyar ta kai kujerar shugabancin yankin Arewa maso Yamma, inda ta zaɓi Tajudeen Abbas, a matsayin ɗan takararta, yayin da Benjamin Kalu daga yankin Kudu maso Gabas, ya samu kujerar mataimaki.
Ana Saura Kiris Ya Bar Ofis, Gwamnan APC Ya Nada Sabbin Kwamishinoni
Da zu rahoto ya zo cewa gwamnan jihar Ebonyi, ya yi naɗin sabbin kwamishinoni ana saura kwanaki kaɗan ya bar ofis.
Gwamna Dave Umahi, ya naɗa sabbin kwamishinoni guda huɗu, yayin da ya rage masa saura kwana 20 ya bar kan kujerar mulki.
Asali: Legit.ng