Bola Tinubu Ya Tafi Nahiyar Turai Kwanaki 19 Gabanin Rantsarwa
- Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya bar Najeriya zuwa nahiyar turai yau Laraba 10 ga watan Mayu, 2023
- Mai magana da yawun zababben shugaban kasan, Tunde Rahman, ya ce Tinubu da tawagarsa zasu gana da masu zuba hannun jari
- A cewarsa, shugaba mai jiran gado zai yi amfani da lokacin zamansa a can wajen tsara bukukuwan bikin rantsarwa
FCT Abuja - Zababben shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya bar Najeriya zuwa nahiyar turai ranar Laraba 10 ga watan Mayu, 2023.
Mai magana da yawun tsohon gwamnan jihar Legas ɗin, Tunde Rahman, ne ya tabbatar da haka a wata sanarwa da ya fitar.
Ya ce shugaban ƙasa mai jiran gado ya bar birnin tarayya Abuja ranar Laraba da tsakar rana tare da tawagar hadimansa mafi kusa da shi.
Legit.ng Hausa ta fahimci cewa sanarwan ta yi bayanin muhimman abu 2 da Tinubu zai maida hankalin yayin zamansa a Turai, na farko tsara bukukuwan rantsarwa da kuma gana wa da masu zuba hannun jari.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Wani sashin sanarwan ya ce:
"Wannam tafiya zata rage wa zababben shugaban kasa yawan damunsa da ake yi gabanin ranar kama aiki 29 ga watan Mayu,"
"Zai yi amfani a zamansa a can wajen tsara shirye-shirye da fidda tsarukan da zai tasa a gaba tare da makunsanta ba tare wasu sun dame su ba."
"A wannan ziyara, zababben shugaban kasa zai gana da masu zuba hannun jari da nufin tallata hajar zuba hannun jari a Najeriya da shirin gwamnatinsa na ba da filin kasuwanci ta hanyar tsaruka da ƙa'idoji."
Bugu da ƙari, Rahman ya ce Tinubu ya jima yana tattauna wa da yan kasuwa a nahiyar turai a fannin noma, fasaha, makamashi da masana'antu.
A cewarsa, zababben shugaban kasa ya jaddara kudurinsa na ganin ya shawo kan yan kasuwar Turai su waiwayo Najeriya, wacce ke shirim tarbansu hannu bibbiyu.
Wutar rikici ta kara ruruwa a majalisar wakilan tarayya
A wani labarin kuma Mun Haɗa Muku Jerin Manyan Majalisun APC 5 da Suka Lashi Takobin Yakar Ɗan Takarar Tinubu a Majalisa Ta 10
Yan majalisun sun nuna rashin jin daɗinsu bisa yadda zababben shugaban kasan ya tsallake su ya zabi Tajudeen Abbas a matsayin wanda yake goyon baya.
Asali: Legit.ng