Tsohon Gwamnan APC Ya Yi Magana Kan Kashin Da Ya Sha a Kotu, Ya Ba Gwamnan PDP Shawara 1 Kwakkwara
- Tsohon gwamnan jihar Osun, Gboyega Oyetola, ya amince da hukuncin kotun ƙoli sannan ya taya gwamna Ademola Adeleke, murna
- Oyetola ya kuma yi kira ga magoya bayansa, ƴaƴan jam'iyyar APC, da waɗanda suka zaɓe shi, da su amince da hukuncin kotun ƙolin
- Ya kuma buƙaci Ademola da ya mayar da hankali wajen yin jagoranci mai kyau, ga mutanen jihar ba tare da la'akari da bambancin siyasa ba
Osogbo, Osun - Gboyega Oyetola, tsohon gwamnan jihar Osun, ya amince da kayan da ya sha bayan kotun ƙoli, ta ayyana wanda ya gaje shi, Ademola Adeleke, a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar na watan Yulin 2022.
A cewar rahoton Tribune, gwamnan cikin wata sanarwa da ya rattaɓawa hannu, ya ce duk da hukuncin kotun ba shi ne abinda magoya bayansa, da ƴaƴan jam'iyyar APC, suka so ba, ya amince da shi domin zaman lafiya da cigaban jihar.
Daga nan Oyetola ya roƙi jam'iyyar APC a jihar, magoya bayansa da waɗanda suka zaɓe shi a lokacin zaɓen gwamnan, da su amince da hukuncin kotun ƙolin a matsayin ƙaddarar ubangiji, cewar rahoton The Cable.
Wani ɓangare na sanarwar na cewa:
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
"Ga ƴaƴan jam'iyyar mu da magoya bayan mu a faɗin jihar nan, ina roƙon ku da ku amince da hukuncin kotun. Wannan abinda ya faru mu nasara ce a gare mu. Nasara ce da rashin nasara ta haɗu a waje ɗaya. Yayin da muka rasa Osun, mun samu Najeriya."
A yayin da ya ke taya gwamna Adeleke, murnar nasarar da ya samu, ya buƙace shi da ya mayar da hankali wajen shugabanci mai kyau, da sauƙe nauyin al'ummar jihar da ke kansa, ba tare da la'akari da bambancin siyasa ko addini ba.
Gwamnan Adeleƙe Ya Yi Magana Kan Nasarar Sa a Kotu, Ya Aike Da Sako Ga APC
A wani rahoton na daban kuma, gwamna Ademola Adeleke, ya yi magana kan nasarar da ya samu a kotun ƙoli, wacce ta tabbatar masa da.nasarar sa
Gwamnan na jihar Osun, ya kuma buƙaci jam'iyyar APC da.ɗan takarar ta da su zo a haɗa hannu tare.domin kai jihar ga tudun mun tsira.
Asali: Legit.ng