Yanzu-Yanzu: Wata Babbar Jam'iyya Ta Janye Karar Da Ta Shigar Kan Nasarar Tinubu

Yanzu-Yanzu: Wata Babbar Jam'iyya Ta Janye Karar Da Ta Shigar Kan Nasarar Tinubu

  • A na dawowa zaman kotu, jam'iyyar Action Peoples Party (APP) ta janye ƙarar ta na ƙalubalantar nasarar Bola Tinubu
  • Jam'iyyar ta hannun lauyanta, Obed Agu, ta buƙaci ta janye ƙarar ne a ranar Laraba 10 ga watan Mayu
  • Lauyoyin Tinubu, hukumar INEC, jam'iyyar APC ba su yi jayayya da buƙatar jam'iyyar na janye ƙarar ba

FCT, Abuja - Jam'iyyar Action Peoples Party (APP) ta janye ƙarar da ta shigar tana ƙalubalantar nasarar Bola Tinubu, a zaɓen shugaban ƙasa na ranar 25 ga watan Fabrairun 2023.

A zaman farko kafin fara sauraron ƙarar a ranar Litinin, lauyan jam'iyyar APP, Obed Agu, ya ce kafin a fara sauraron ƙarar jam'iyyu za su iya zaɓar sulhunta kansu, cewar rahoton The Cable.

Jam'iyyar APP ta janye karar da ta shigar kan Tinubu
Shugaba Buhari tare da Bola Tinubu a wajen kamfe Hoto: Bola Tinubu
Asali: Twitter

Ya bayyana cewa, waɗanda ake ƙarar, Tinubu da jam'iyyar All Progressives Congress (APC) da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC), su yarda da abinda mai shigar da ƙara ya gabatar duba da girman abin da aka shigar da su ƙara a kai.

Kara karanta wannan

Majalisa Ta 10: Manyan Dalilai 2 Da Suka Sanya Bola Tinubu Goyon Bayan Akpabio

Daga nan sai kotun ta ɗage sauraron ƙarar zuwa rana Laraba, domin ci gaba da fara sauraron ta.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sai dai, bayan kotun ta dawo zamanta, Agu ya buƙaci ya janye ƙarar, rahoton Vanguard ya tabbatar.

Lauyan hukumar INEC, Abubakar Mahmoud, lauyan Tinubu, Wole Olanipekun, da lauyan APC, Lateef Fagbemi, ba su yi jayayya da buƙatar sa ta janye ƙarar ba.

A dalilin hakan sai kotun ta yi watsi da ƙarar.

Shugaban Majalisa: Sanatoci 18 Sun Botsarewa APC, An Fito da ‘Yan Takara Daban

A wani rahoton na daban kuma, wasu zaɓaɓɓun sanatocin jam'iyyar All Progressives Congress (APC), sun yi fito na fito da matsayar jam'iyyar kan shugabancin majalisa ta 10.

Sanatocin guda 18 sun ce sam ba su gamsu da zaɓen da APC ta yi wa sanata Godswill Akpabio da Barau Jibrin ba, a matsayin waɗanda za su jagoranci majalisar dattawa ta 10.

A dalilin hakan sanatocin sun shirya yi wa jam'iyyar bore inda za su marawa wasu ƴan takara daban baya, ba.zaɓin APC ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng