Atiku da Gwamna Wike Zasu Hadu a Wurin Taron Gwamnonin PDP a Abuja

Atiku da Gwamna Wike Zasu Hadu a Wurin Taron Gwamnonin PDP a Abuja

  • Kungiyar gwamnonin PDP ta shirya taro na musamman kan shugabanci nagari a birnin tarayya Abuja
  • Ana tsammanin gwamnoni masu barin gado da kuma zababbu zasu halarci wurin taron ranar Alhamis
  • Haka nan ana tsammanin Atiku Abubakar da gwamna Wike zasu haɗu da juna tun bayan zaben 2023

Abuja - Ana tsammanin tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, da gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas zasu halarci taron da ƙungiyar gwamnonin PDP ta shirya.

Gwamnan jihar Sakkwato kuma shugaban ƙungiyar, Aminu Tambuwal, ne mai karban baƙin da zasu halarci taron wanda aka tsara gudanarwa a Transcorp Hilton, Abuja ranar Alhamis.

Atiku da gwamna Wike.
Atiku da Gwamna Wike Zasu Hadu a Wurin Taron Gwamnonin PDP a Abuja Hoto: thecable
Asali: UGC

Darakta janar na kungiyar gwamnonin PDP, C.I.D Maduabum, ya ce masani kan tattalin arziki, Muda Yusuf, zai yi lakca a wurin taron, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Shugaba Mai Jiran Gado, Bola Tinubu Zai Ƙara Tafiya Ƙasar Waje? Gaskiya Ta Bayyana

Ya ce masanin zai yi jawabi kan, "Shugabanci na gari a matakin jiha: Batutuwa, abinda ake tsammani da zahirin sakamako."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Wannan taro wata dama ce ga shugabannin PDP, masu ruwa da tsaki da mambobi su haɗu a inuwa ɗaya tun bayan kammala babban zabe," inji DG.

Gwamnonin da zasu halarci taron

Ana tsammanin baki ɗaya gwamnoni masu barin gado da zababbun gwamnonin da za'a rantsar ranar 29 ga watan Mayu, 2023, za su halarci taron.

Zababbun gwamnonin da ake sa ran ganinsu a wurin taron sun ƙunshi, Seyi Makinde na jihar Oyo, Umo Bassey Eno na Akwa Ibom, Peter Ndubusi Mbah na Enugu, da Agbu Kefas na jihar Taraba.

Sauran sun haɗa da, Siminalayi Fubara na jihar Ribas, Sheriff Oborevwori na jihar Delta, Dauda Lawal na jihar Zamfara da kuma Caleb Mutfwang na jihar Filato.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Atiku Abubakar, Peter Obi, Ayu da Gwamnan G-5 Sun Haɗu a Wuri Ɗaya, Bayanai Sun Fito

Haka nan mambobin kwamitin gudanarwa (NWC), mambobin kwamitin zartaswa (NEC) da amintattun jam'iyyar PDP (BoT) zasu halarci taron a Abuja.

Atiku zai haɗu da gwamna Wike

Da yuwuwar Atiku da gwamna Wike zasu haɗu su gana da juna a wurin taron, karon farko tun bayan babban zaben shugaban kasa ranar 25 ga watan Fabrairu, 2023.

Tun lokacin da Atiku ya lashe tikitin takarar shugaban ƙasa a inuwar PDP, gwamna Wike ya ɓalle, ya jagoranci fafutukar, "Mulki ya koma kudu," tare da wasu gwamnonin PDP 4.

A wani labarin kuma Mun tattaro muku Jerin Manyan Majalisu 5 na APC da Suka Lashi Takobin Yakar Ɗan Takarar Tinubu a Majalisa Ta 10

Tun bayan sanarwan jam'iyyar APC, wutar rikici ta ɓullo a tseren neman shugabancin majalisar wakilan tarayya.

A yanzun, manyan jiga-jigan yan majalisa 5 a inuwar APC, sun ja tunga, sun ce ba zasu yi wa zabin Tinubu mubaya'a ba.

Kara karanta wannan

Gaskiya Ta Bayyana Kan Dalilin Gwamnonin Arewa Na Goyon Bayan Bola Tinubu

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262