A Kai Kasuwa: Kujerar Minista 1 Da Ba Zan Karba a Gwamnatin Tinubu Ba, El-Rufai
- Gwamnan jihar Kaduna ba zai amince ya sake zama Ministan birnin tarayya a mulkin Bola Tinubu ba
- Nasir El-Rufai ya taka rawar gani wajen zaman Bola Tinubu shugaban kasa, tun daga samun takara a APC
- Tsakanin 2003 da 2007, El-Rufai ya rike wannan kujera, ya ce a yanzu ya girmi ya sake rike matsayin
Abuja - Malam Nasir El-Rufai, ya ce ba zai karbi matsayin Ministan babban birnin tarayya a gwamnatin Bola Tinubu ba, ya kuma bada dalilansa.
Daily Trust ta ce ana rade-radin Nasir El-Rufai zai iya zama Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa ko Ministan Abuja a gwamnati mai zuwa.
Gwamnan mai barin gado ya musanya jita-jitar, yana cewa bai neman wadannan mukamai.
Da yake jawabi a wajen kaddamar da wani littafi a garin Abuja, El-Rufai ya nuna aikinsa ya kare, babu abin da zai hada shi da kujerar da ya bari, Daily Post ta ruwaito.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
El-Rufai: "Nayi kuma na gama."
"Na yi aiki na, na gama, ba na hangen baya. Asali ma a lokacin da na bar birnin Abuja, lokacin da na sake ziyartar Abuja kurum shi ne a 2016.
A lokacin an nada abokina tun sakandare a matsayin Ministan, ya nemi ya gana da ni, sai na je.
Da zarar na bar aiki, ba na waiwaye. Idan na bar Kaduna nan da kwanaki 19, ko ziyara ba zan je ba sai idan ya zama dole, ban tunanin Abuja.
Ni nayi bangaren da zan yi, ba na maganar kokarin wadanda za su shiga ofis a baya na.
Ko an yi mani tayi, ba zan zo Abuja ba. Kamar yadda na fada ba na maimaita aji kuma akwai wadanda zan iya bada shawarar a ba kujerar.
A shekaruna, na tsufa da fama da rushe-rushe, a nemi matashi mai jini a jika ko kuma matashiyar mace.
Waziri Adio ya gayyato Malam
Jaridar ta ce wata tsohuwar cibiyar Amurka da aka kafa domin wanzar da zaman lafiya ta shirya taron da hadin wata kungiya da ke garin Abuja.
Tsohon shugaban Hukumar NEITI, Waziri Adio ya kafa kungiyar Agora Policy, aka gayyaci tsohon Minista birnin tarayyar domin bada gudumuwa.
Takarar Godswill Akpabio a majalisa
An ji labari wani jigo a AFC, Musa Sa'ido ya fito yana cewa su ne su ka san wanene Godswill Akpabio domin su ne 'Yan Arewa mazauna yankin Kudu.
Saidu ya ce Sanata Godswill Akpabio bai cikin masu kaunar mutanen Arewacin Najeriya, don haka ya nuna bai goyon ya zama shugaban majalisa.
Asali: Legit.ng