Manyan Majalisun APC 5 da Suka Lashi Takobin Yakar Ɗan Takara Tinubu a Majalisa Ta 10

Manyan Majalisun APC 5 da Suka Lashi Takobin Yakar Ɗan Takara Tinubu a Majalisa Ta 10

Mai yuwuwa jam'iyyar APC na tunanin ta kawo karshen rige-rigen neman kujarar kakakin majalisa wakilan tarayya yayin da ta ayyana Tajudeen Abbas daga Kaduna a matsayin wanda take goyon baya.

Amma ga dukkan alamau hakan ya ƙara kunna wuta a jam'iyya mai mulki domin manyan jiga-jigan 'yan majalisu 5 sun sha alwashin kalubalantar zaɓin da jam'iyyarsu ta yi.

Shugabancin majalisa ta 10.
Manyan Majalisun APC 5 da Suka Lashi Takobin Yakar Ɗan Takara Tinubu a Majalisa Ta 10 Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Idan baku manta ba a wata sanarwa da kakakin APC na ƙasa, Felix Morka, ya fitar ranar Litinin, ya ce jam'iyya ta cimma matsaya ne bayan ta nemi shawarin Bola Tinubu.

Jim kaɗan bayan wannan sanarwa, jiga-jigan 'yan majalisu 5 na APC karkashin jagorancin mataimakin kakakin majalisar, Idris Wase, suka lashi takobin yaƙar wanda APC ta zaɓa.

Legit.ng Hausa ta tattaro muku 'yan majalisun da suka sha alwashin faɗa da zaɓin APC, gasu kamar haka:

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Shugaba Mai Jiran Gado, Bola Tinubu Zai Ƙara Tafiya Ƙasar Waje? Gaskiya Ta Bayyana

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

1. Idris Wase

Wase ne mataimakin kakakin majalisar wakilan tarayya ta 9 kuma ya bayyana sha'awar nemnan kujarar kakakin majalisa mai zuwa ta 10.

Ɗan siyasan, haifaffen jihar Filato ya kammala karatu a makarantar Harvard Kennedy School of Government da ke ƙasar Amurka, Premium Times ta rahoto.

2. Muktar Betara

Honorabul Batara, mamba mai wakiltar mazaɓar Biu/Bayo/Shani da Kwaya Kusar a majalisar wakilan tarayya daga jihar Borno, shiyyar arewa maso gabashin Najeriya.

Ya samu nasarar lashe zaben da ya ba shi damar shiga majalisar wakilan tarayya karon farko a shekarar 2007.

3. Sada Soli

Sada Soli ya yi aiki a matsayin ma'aikaci a majalisar tarayya tsawon shekaru 14 daga bisani ya tsunduma siyasa a shekarar 2007. Shi ne mai wakiltar Jibiya da Kaita daga Katsina.

Ya ayyana burinsa na neman kujarar shugaban majalisar wakilan tarayya wacce zata fara aiki a wata mai zuwa, kamar yadda Guardian ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Jam'iyyar APC Ta Sanar Da Wadanda Za Su Shugabanci Majalisa Ta 10

4. Alhassan Ado Doguwa

Yanzu haka Doguwa ne shugaban masu rinjaye a majalisar wakilan tarayya kuma tuni ya shiga tseren kujerar kakakin majalisar. Yana cikin waɗanda zasu ja daga da Tinubu.

Ɗan majalisa mai wakiltar Doguwa da Tudun Wada na jihar Kano, yana fama da tuhumar kisan mutum 3 lokacin zaɓen shugaban ƙasa da yan majalisun tarayya.

5. Aminu Sani Jaji

Tsohon shugaban kwamitin fasaha da harkokin tsaron cikin gida na majalisar wakilai, Sani Jaji, ya ayyana shiga tseren kujerar kakakin majalisa ta 10.

Jaji, ɗan kimanin shekara 49 mai wakiltar mazaɓun Ƙauran Namoda/Birnin Magaji na jihar Zamfara, ya samu nasarar komawa majalisa karo na biyu kenan idan an rantsar da su a watan Yuni.

Muna Maraba da Gwamna Wike Idan Ya Yanke Dawowa APC, Jigo

A wani labarin kuma Babban Jigon APC ya ce a duk lokacin da gwamna Wike ya yanke shawarin sauya sheƙa daga PDP, zasu karɓe shi hannu biyu

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Rikicin Jam'iyyar Adawa Ya Kara Tsanani, Ta Dakatar da Manyan Jiga-Jigai 3

Chief Tony Okocha, ya jinjina wa gwamna Wike bisa ayyukan da ya zuba wa talakawan jihar Ribas, a cewarsa ba'a taba gwamna kamarsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262