A Karon Farko Shugaba Buhari Ya Yi Magana Kan Nasarar Da Gwamnan PDP Ya Samu a Kotu

A Karon Farko Shugaba Buhari Ya Yi Magana Kan Nasarar Da Gwamnan PDP Ya Samu a Kotu

  • Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya nemi al'ummar jihar Osun da su ba gwamnan jihar dukkanin haɗin kan da ya dace
  • Shugaban ya yi nuni da cewa gwamnan na buƙatar haɗin kan mutanen jihar domin ciyar da ita gaba
  • Gwamna Ademola Adeleke ya sake samun nasara a kotun ƙoli, inda ta tabbatar da shi a matsayin gwamnan jihar Osun

Abuja - Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya buƙaci al'ummar jihar Osun da su haɗa kai da gwamna Ademola Adeleke, wajen ciyar da jihar gaba.

Channels tv ta kawo rahoto cewa kakakin shugaban ƙasa, Femi Adesina, a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, ya ce shugaban ƙasar ya yi na'am da hukuncin kotun ƙolin kan zaɓen gwamnan jihar Osun na ranar 16 ga watan Yulin 2022.

Buhari ya nemi mutanen Osun su ba Ademola haɗin kai
Shugaban kasa Muhammadu Buhari da Ademola Adeleke Hoto: Channelstv.com
Asali: UGC

Shugaban ƙasar ya kuma nuna muhimmancin fannin shari'a wajen ƙara ƙarfafa doka da dimokuraɗiyya.

Kara karanta wannan

Gaskiya Ta Bayyana Kan Dalilin Gwamnonin Arewa Na Goyon Bayan Bola Tinubu

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Da hukuncin ƙarshe na kotun ƙoli, shugaban ƙasa yana tunatar da ƴan siyasa da magoya bayan su cewa, abu mafi muhimmanci shine sanya mutane jin amfanuwa da shugabanci mai kyau, domin tabbatar da samuwar jihar Osun mai cike da cigaba da zaman lafiya."
"Shugaban ƙasar ya kuma buƙaci al'ummar jihar musamman manya daga cikin su, su ba gwamnatin Ademola Adeleke dukkanin goyon bayan da ta ke buƙata domin tabbatar da samun nasarar dukkanin wasu shirye-shirye, tsare-tsaren da aka yo domin al'umma."
"Kamata ya yi a riƙa kallon zaɓuka a matsayon hanyar da za ta ɓulle, wanda shine samun cigaban al'umma cikin yanayin kwanciyar hankali, ba wai ɓaɓatu ba. Yanzu lokacin tafiya da kowane a jihar bayan an kawo ƙarshen shari'a."

Lauyan Abba Gida-Gida Ya Yi Maganar Yiwuwar Samun Nasarar APC da Gawuna a Kotu

Kara karanta wannan

Yadda Kasar Masar Ta Umarci Ɗaliban Najeriya Sama da 500 Su Koma Sudan Kan Halayyar Mutum 2

A wani rahoton na daban kuma, lauyan da ya ke kare nasarar Abba Gida-Gida da jam'iyyar NNPP a kotu, ya yi magana kan yiwuwar samun nasarar jam'iyyar APC a kotu.

Bashir Yusuf Muhammad Tudun Wazirci, yana ganin sam masu ƙalubalantar nasarar Abba Gida-Gida, ba su kama hanyar yin nasara a kotu ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng