Muna Maraba da Gwamna Wike Idan Ya Yanke Dawowa APC, Jigo

Muna Maraba da Gwamna Wike Idan Ya Yanke Dawowa APC, Jigo

  • Jigon jam'iyyar APC a jihar Ribas yace zasu yi maraba da gwamna Wike idan har ya yanke shawarin ficewa daga PDP
  • Chief Tony Okocha, ya ce Wike na ɗaya daga cikin waɗanda suka ba da gudummuwa har Tinubu ya lashe zaɓen 2023
  • Ya kuma yaba da irin ayyukan raya ƙasa da gwamna Wike ya zuba a jihar Ribas, ya ce tarihi ba zai manta da gwamnan ba

Rivers - Jigon jam'iyyar APC, Chief Tony Okocha, ya bayyana cewa zasu karbi gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, hannu bibbiyu idan ya zaɓi ficewa daga PDP.

Jaridar Leadership ta rahoto cewa Chief Okocha ya yi wannan furucin ne yayin da yake hira da manema labarai a Patakwal, babban birnin jihar Ribas.

Gwamna Nyesom Wike.
Muna Maraba da Gwamna Wike Idan Ya Yanke Dawowa APC, Jigo Hoto: Nyesom Wike
Asali: Facebook

Ya ayyana gwamna Wike a matsayin ɗaya daga cikin jiga-jigan da suka taka rawa wajen naɗa tsohon gwamnan Legas, Bola Tinubu a matsayin zababben shugaban ƙasa.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Shugaba Mai Jiran Gado, Bola Tinubu Zai Ƙara Tafiya Ƙasar Waje? Gaskiya Ta Bayyana

A kalamansa, Okocha ya ce:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"A yau zamu ce gwamna Wike na ɗaya daga cikin waɗanda suka taimaka wajen samun nasarar zababben shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu."
"Idan Wike na son dawowa jam'iyyar APC, zamu yi maraba da shi, amma abu ɗaya da nake tsoro, bana son Najeriya ta zama ƙasar jam'iyya ɗaya tal."

Ba'a taba gwamna kamar Wike ba a Ribas - Okocha

Jigon ya musanta cewa ya koma bayan Wike ne yake kokarin kare shi, inda ya ayyana gwamnan a matsayin wanda ya fi kawo ci gaba a fili a tarihin jihar Ribas.

Jigon ya ci gaba da cewa:

"Ba wai ina kare gwamna Wike bane, amma idan ana batun ayyaukan raya kasa da zasu kawo ci gaba a jihar Ribas, babu kamar Wike."

Ya kuma jaddada cewa ɗan takarar gwamna a inuwar APC na jihar, Tonye Cole, bai ba da gudummuwar ko kwandala ba wajen shirya ralin kamfen shugaban ƙasa.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Atiku Abubakar, Peter Obi, Ayu da Gwamnan G-5 Sun Haɗu a Wuri Ɗaya, Bayanai Sun Fito

Kotun Koli ta yanke hukunci kan zaben gwamnan Osun

A wani labarin kuma Kotun Koli Ta Tabbatar ɗa Nasarar Gwamna Adeleke a Zaben Jihar Osun

Kotun Allah ya isa ta kori karar da tsohon gwamna jihar Osun, Oyetola na jam'iyyar APC ya kalubalanci nasarar PDP a zaben watan Yuli, 2022.

Oyetola ya yi zargin cewa PDP ta yi aringizon kuri'u amma Kotu ta ce ya gaza gabatar da hujjoji masu karfi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262