Tinubu Zai Sake Tafiya Zuwa Wata Kasar Waje? Hadiminsa Ya Bayyana Gaskiya

Tinubu Zai Sake Tafiya Zuwa Wata Kasar Waje? Hadiminsa Ya Bayyana Gaskiya

  • Zababben shugaban kasa, Asiwaju Bola Tinubu, ya shirya tafiya ƙasar waje amma ba'a bayyana ainihin ranar da zai tafi ba
  • Mai magana da yawun Tinubu, Mista Tunde Rahman, ya tabbatar da haka ranar Litinin 8 ga watan Mayu, 2023
  • Tsohon gwamnan Legas ɗin zai bar Najeriya ne domin guje wa matsin lamba kan waɗanda zasu shugabanci majalisa ta 10

Abuja - Zababben shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, zai sake kakkaɓe takalmansa ya fice daga ƙasar nan, kowane lokaci daga yanzu.

Hadimin shugaba mai jiran gado, Tunde Rahman, ne ya tabbatar da lamarin ga jaridar Leadership da daren ranar Litinin 8 ga watan Mayu, 2023.

Bola Tinubu.
Tinubu Zai Sake Tafiya Zuwa Wata Kasar Waje? Hadiminsa Ya Bayyana Gaskiya Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Tinubu na shirin yin tafiya, hadiminsa ya tabbatar

Rahman ya ce:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

Cikakken Jerin Sunayen Manyan Alƙalai 5 da Zasu Jagorancin Shari"a Kan Zaben Tinubu a 2023

"Da yuwuwar shugaban kasa mai jiran gado, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, zai sake saɓa jakarsa zuwa wata ƙasar waje, amma ina da tabbacin ba gobe (Talata) zai tafi ba."

Bayanai sun nuna cewa tsohon gwamnan jihar Legas ɗin zai yi wannan tafiya ne domin guje wa Dirama da rikicin da ka iya biyo baya bayan raba muƙaman majalisar tarayya ta 10.

APC ta fitar da sanarwa a hukumanci kan shugabancin majalisa ta 10

Idan baku manta ba Legit.ng Hausa ta kawo muku rahoton yadda jam'iyyar APC ta raba kujerun shugabannin majalisar tarayya ta 10 zuwa wasu shiyyoyi.

A hukumance, jam'iyyar APC ta sanar da sunan Sanata Godwill Akpabio a matsayin wanda ta zaɓa ya yi takarar kujerar shugaban majalisar dattawa ta 10.

Haka zalika, jam'iyya mai mulki ta zaɓi Abbas Tajudden, ɗaya daga cikin jiga-jigan yan majalisar wakilai, a matsayin wanda take goyon bayan ya zama kakakin majalisa ta 10.

Kara karanta wannan

Buhari: Abin da Ya Sa Na Ki Fitowa Karara In Goyi Bayan Magajina a Zaben Gwanin APC

Bayan kammala babban zaben 2023, Jam'iyyar APC ce kan gaba a yawan mambobin majalisar tarayya wacce zata kama aiki nan da wasu makonni.

Manyan jiga-jigan PDP da suka rarrabu sun sake haɗuwa

A wani labarin kuma Peter Obi, Atiku Abubakar, Ayu da Gwamna Makinde Sun Hadu a Wurin Jana'iza

Manyan jiga-jigan jam'iyyar PDP da suka watse gabanin zsben 2023 sun gana da juna a wurin jana'izar mahaifin gwamnan Bayelsa, Douye Diri.

Peter Obi, wanda ya bar PDP tun gabanin zaɓen fidda gwani, Atiku Abubakar, gwamna Makinde, mamban G-5, da sauran jiga-jigai sun halarci wurin jana'izar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262