Har An Soma Zargin Tinubu da Rashin Adalci Tun Kafin Hawa Mulki Kan Takarar Majalisa

Har An Soma Zargin Tinubu da Rashin Adalci Tun Kafin Hawa Mulki Kan Takarar Majalisa

  • Sanatoci masu-ci da zababben Sanatoci daga Jihohin Kudu maso gabas sun yi taro a kan zaben Majalisar kasa
  • ‘Yan siyasar yankin Ibo sun nuna babu abin da zai sa su marawa Godswill Akpabio baya, ya samu mukami
  • An yi kira zuwa ga Bola Tinubu ya yi adalci, a tabbata Ibo ya zama shugaban majalisar dattawa a yanzu

Abuja - Wasu Sanatoci masu-ci da zababben Sanatocin yankin Kudu maso gabas ba su gamsu Godswill Akpabio ya zama shugabansu a majalisa ba.

A rahoton da aka samu daga Premium Times, an fahimci wadannan ‘Yan siyasa sun yi taro a garin Abuja a ranar Lahadi, suka cin ma wannan matsaya.

Sanatocin da masu jiran gado 11 a majalisar dattawa sun sa hannu cewa yi wa Godswill Akpabio mubaya’a, yana nufin an maida su saniyar ware.

Kara karanta wannan

Bai Kaunar Mu: Dattawan Arewa Sun Hango Hadari a Zaman Akpabio Shugaban Majalisa

Tinubu
Bola Tinubu a jirgin sama Hoto: @SpeakerGbaja
Asali: Facebook

‘Yan majalisar su na ganin ba a damawa da ‘yan yankin Kudu maso gabas a siyasa, suka ce tun 1966 aka hana wani daga yankinsu zama shugaban kasa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Hausawa-Yarbawa-Inyamurai

Abin da Sanatocin da sauran ‘Yan siyasar na bangaren Ibo su ke so shi ne Sanata Akpabio ya ajiye maganar takara, ya goyi bayan wani daga yankin na su.

‘Yan majalisar sun nuna a yadda ake tafiya, ba a yi wa bangarori adalci wajen raba mukamai ba.

Yayin da Bayarabe zai zama shugaban kasa a karshen Mayun 2023, Arewa ta samu kujerar mataimakin shugaban kasa, su na so na uku ya zama Ibo.

"Mu na so zababben shugaban kasa ya yi la’akari da halin da Najeriya ta ke ciki, ya tabbatar da cewa an gina kasar nan a kan adalci da gaskiya tsakanin Hausawa, Ibo da Yarbawa.

Kara karanta wannan

Majalisa Ta 10: Tinubu Ya Ayyana Wadanda Yake So, Yari Ya Ce Zababben Shugaban Kasar Ya Yi Kadan

“A wannan gaba, gaba daya mun amince za mu goyi bayan ‘yan takaran Kudu maso gabas a APC, za mu jajirce kuma mun fara hada-kai da sauran zababbun Sanatoci a kan hakan.”

- Sanatocin Kudu maso gabas

Sun ta ce Ifeanyi Ubah mai wakiltar Kudancin Anambra ya karanto matsayar da aka dauka.

A madadin sauran jagororin siyasar Kudu maso gabas, Sanata Ifeanyi Ubah ya ce abin da ya kamata ayi shi ne a kawo zaman lafiya ba akasin haka ba.

Abin da ya ke tinkaho da shi, shi ne ya taba zama ‘dan majalisa, sannan ya fi shekaru 35 yana siyasa kuma har gobe ana yi masa kallon mutum mai kima.

Patrick Ndubueze ya fito

Duk da Dave Umahi ya janye, rahoto ya nuna mutum uku sun fito neman shugabanci daga Kudu maso gabas, daga ciki har da Hon. Patrick Ndubueze.

Patrick Ndubueze ya shiga takarar shugaban majalisar dattawa, ya kuma sanar da shugabannin APC na kasa cewa yana goyon bayansu a takararsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng