Kotun Ƙarar Zaɓe: Atiku Ya Buƙaci A Haska Zaman Kotun Kai Tsaye A Talabijin
- Ɗan takarar shugabancin ƙasa na PDP Atiku Abubakar ya roƙi kotu ta bada dama a haska shari'ar da za a gudanar kai tsaye a gidajen talabijin
- Atiku ya ce ko wane ɗan ƙasa da ya fito ya yi zaɓe ya na da haƙƙin ganin yadda shari'ar take kayawa
- Atiku ya kuma buƙaci kotu ta karɓe satifiket ɗin da ta ba wa Tinubu domin kuwa a cewar shi Tinubu bai cika sharuddan cin zabe ba
Abuja - Ɗan takarar shugabancin ƙasa na jam'iyyar PDP a zaɓen da ya gabata Alhaji Atiku Abubakar ya roƙi da a haska zaman kotun ƙarar da ya kai Bola Tinubu na APC kai tsaye a gidajen talabijin na ƙasar nan.
A yau Litinin, 8 ga watan Mayu ake sa ran fara sauraron ƙarar da Atiku Abubakar ya shigar da Tinubu na ƙalubalantar sakamakon zaben shugaban kasa na bana da aka yi a watan Faburairu
Lauyoyin Atiku sun miƙa buƙata gaban kotu
Kamar yadda Legit ta samu bayanai, lauyoyin Atiku Abubakar ne bisa jagorancin Chris Uche SAN, suka aikewa kotun da wannan buƙata ta barin 'yan jarida su haska shari'ar kai tsaye a yayin da ake gudanar da ita.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Atiku ya ce dalilin da ya sa suka buƙaci a haska shari'ar kai tsaye shine saboda abu ne da ya shafi 'yan ƙasa baki ɗaya saboda haka akwai buƙatar su kalli abinda ke faruwa kai tsaye.
Ya ƙara da cewar 'yan ƙasa, waɗanda su ne suka fito suka yi zaɓe, suna da haƙƙin sanin duk abinda ke faruwa kai tsaye kamar yadda masu ruwa da tsaki a zaɓukan ma ke da alhakin hakan Vanguard ta ruwaito.
Lauyoyin Atiku sun buƙaci a kwace satifiket ɗin Tinubu
Atiku ya ce duba da yadda aka samu cigaba a ɓangaren fasahohin zamani ta yadda ko daga ina mutum zai iya samun damar sauraron shari'ar .
Ya kuma bayyana yaƙinin cewa kotun ta riga da ta karɓi cigaban zamani don haka ya ga dacewar a bari a haska shari'ar kai tsaye domin kowa ya samu damar ganin yadda za a gudanar da shari'ar cikin adalci.
Lauyoyin Atiku sun kuma buƙaci hukumar zaɓe wato INEC, da ta karɓe takardar shaidar cin zaɓen da ta ba wa Tinubu saboda a cewarsu sanar da lashe zaɓen na shi da aka yi bai cika sharuɗɗan da doka ta tanada ba kamar yadda Punch ta wallafa.
'Yan adawa za su iya karɓe kujerar Tinubu idan sun cika sharuɗɗa
A wani labarin mai alaƙa da wannan kunji wani lauya da ya fito ya bayyana cewa 'yan adawa za su iya karɓe nasarar da Tinubu ya yi a idan har za su iya kare hujjojin su a gaban kotu.
Lauyan mai suna Festus Ogun ya kuma ja hankalin masu bugun ƙirjin cewa ba za a rantsar da Tinubu ba a ranar 29 ga watan Mayu da muke ciki kan cewa su daina domin hakan ba shi a cikin doka.
Asali: Legit.ng