Ana Dab Da Rantsar Da Tinubu, Wata Kungiya Tace a Dakata
- Yayin da ranar da za a rantsar da Bola Tinub ke ƙara matsowa wata ƙungiyar Inyamurai ta ce a dakata
- Ƙungiyar ta buƙaci da kada a rantsar da Bola Tinubu har sai an kammala sauraron ƙararrakin da ke ƙalubalantar nasarar sa
- Ƙungiyar ta kuma nemi da a tabbatar an yi adalci wajen yanke hukunci kan ƙalubalantar nasarar da Tinubu ya samu
Abuja - Wata ƙungiyar Inyamurai mai suna Igbo Youth Patriotic Forum, ta buƙaci alƙalin alƙalai na ƙasar nan, da kada ya rantsar da zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Bola Tinubu, har sai an kammala sauraron ƙararrakin da ke ƙalubalantar nasarar sa a kotu.
Nasarar Bola Tinubu a zaɓen shugabam ƙasa na ranar Asabar, 25 ga watan Fabrairun 2023, na shan ƙalubalanta a gaban kotu.
Daily Trust tace shugaban ƙungiyar, Cif Simon Okeke, ya bayyana cewa ƙararrakin da ake yi kan hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) kan ayyana Bola Tinubu, za a iya sauraron su da gaggawa kafin a rantsar da shi, inda ya ƙara da cewa idan har hakan bai samu ba, za a iya ɗage rantsar da shi.
Majalisa ta 10: Kakaba Shugabannin Majalisar Wakilai Ya Kawo Rudani a APC, Wasu 'Yan Takara Sun Yi Bore
A kalamansa:
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
"Kundin tsarin mulkin ƙasar nan bai ce dole sai an rantsar da shugaban ƙasa ba a ranar 29 ga watan Mayu. Don haka, mu bari ɓangaren shari'a ya yi aikin sa."
“Saboda haka mu na kira da ɓangaren shari'a na ƙasar nan, da ya yi la'akari da abin da miliyoyin ƴan Najeriya su ke so, da kuma cigaba da wanzuwar Najeriya, wajen sauraron waɗannan ƙararrakin domin kaucewa rashin yin adalci wanda zai iya kawo ɓarkewar rikici a ƙasar nan."
Gaskiya Ta Bayyana Kan Dalilin Gwamnonin Arewa Na Goyon Bayan Bola Tinubu
A wani rahoton na daban kuma, kun ji yadda shugaban ƙungiyar gwamnonin Arewacin Najeriya ya bayyana dalilin su, na goyon bayan Bola Tinubu.
Simon Lalong na jihar Plateau, ya bayyana cewa adalci da gaskiya ne ya sanya suka ce tilas sai mulki ya koma Kudancin Najeriya, inda daga ƙarshe, Bola Tinubu ya samu nasarar lashe zaɓen shugaban ƙasa, a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar APC.
Asali: Legit.ng