Majalisar Tinubu: Ba Na Kamun Kafa Don Samun Mukamin Shugaban Ma’aikata – El-Rufai
- Gwamnan jihar Kaduna ya magantu kan rade-radin da ke yawo cewa yana zawarcin kujerar shugaban ma'aikatan shugaban kasa
- Gwamna Nasir El-Rufai ya ce shi ci gaban kasar yake so ba wai mukaman gwamnati ba
- Ya kuma ce bayan kammala wa'adin mulkinsa a ranar 29 ga watan Mayu zai koma gefe ya dunga bayar da shawarwari a duk sanda bukatar hakan ta taso
Gombe - Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya yi watsi da rade-radin cewa yana kamun kafa domin samun mukamin shugaban ma'aikatan shugaban kasa a majlisar Sanata Bola Tinubu.
El-Rufai ya bayyana hakan ne a Gombe a ranar Asabar, 6 ga watan Mayu yayin da yake jawabi ga manema labarai, rahoton Vanguard.
Rahotanni sun yi ikirarin cewa El-Rufai ya kasance a jihar ne don kaddamar da rukunin gidaje 550 da cibiyar sadarwa ta GOGIS.
Gwamna Umahi Ya Hakura Da Takarar Kujerar Shugaban Majalisar Dattawa, Ya Ayyana Goyon Bayansa Ga Wani Dan Takara
Ya bayyana rahotannin da aka dunga yadawa da wallafawa a jaridun kasar a matsayin 'hasashe kawai'.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Na fi son ci gaban Najeriya fiye da mukami, El-Rufai
Gwamnan ya ce ya fi mayar da hankali wajen ba da gudunmawa ga ci gaban Najeriya fiye da zawarcin mukamai.
El-Rufai ya bayyana cewar kasancewa a cikin gwamnati ba shine hanya guda da mutum zai bayar da gudunmawa ga ci gaban Najeriya ba, cewa koda baya a cikin gwamnati, zai ci gaba da jajircewa kan ci gaban kasar.
Daily Post ta nakalto El-Rufai yana cewa"
"Ban yi wannan tattaunawar da zababben shugaban kasa ba kuma ba na son rade-radi.
"Na karanta a jaridu nau'in ayyuka iri-iri da aka bani amma kun sani, ni jajirtaccen dan Najeriya ne.
"Ina son ganin kasata ta ci gaba kuma zan yi duk abun da zan iya don bayar da gudunmawa ga ci gaban kasar nan.
“Za Su Kashe Ni”: Matashin Da Aka Yi Safarar Sassan Jikinsa Ya Roki Gwamnatin Birtaniya Ta Ba Shi Mafaka
"Amma, ba sai ina cikin gwamnati zan aikata haka ba. Duk wanda ke aiki a ma'aikata mai zaman kanta ko kungiyar jama'a yana bayar da gudunmawa.
"Ba wata hanya daya da zai bayar da gudunmawa ga kasar kuma ba zan daina aiki don ci gaban Najeriya ba."
Gwamnan ya ce yayin da zai bar mulki a ranar 22 mai zuwa, zai karbi hutu amma zai kasance a kasa don bayar da shawara a inda bukatar hakan ta taso kan yadda za a ciyar da kasar gaba.
Kan shugabancin Tinubu daga ranar 29 ga watan Mayu, El-Rufai ya ce Najeriya ba za ta yi danasanin zabar zababben shugaban kasa ba, yana mai cewa ranakun jin dadi na nan zuwa karkashin gwamnatin Tinubu.
Shugaban majalisar dattawa ta 10: Yari ya yi watsi da Tinubu, ya ki janyewa Akpabio
A wani labari na daban, tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari ya ki hakura ya janye daga tseren kujerar shugaban majalisar dattawa.
Asali: Legit.ng