Labour Party a Kaduna Ta nesanta kanta da tsagin Apapa, Ta Dakatar da jiga-jigai 3
- Jam'iyyar Labour Party reshen jihar Kaduna ta nesanta kanta daga tsagin shugabancin Lamidi Apapa a matakin ƙasa
- Bayan wani taron gaggawa da ta gudanar, LP ta yanke dakatar da wasu manyan jiga-jigai uku bisa zargin cin amana
- LP ta shiga rikici ne tun bayan da Kotu ta hana Julius Abure, ayyana kansa a matsayin shugaban jam'iyya na ƙasa
Kaduna - Rigingimun cikin gida da suka addabi jam'iyyar LP ya buɗe sabon shafi yayin jam'iyyar reshen jihar Kaduna ta nesanta kanta da tsagin Lamidi Apapa.
Haka nan kuma jam'iyyar ta dakatar da wasu manyan jiga-jiganta uku bisa zargin cin amana da zagon ƙasa, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Tun a wurin taron majalisar zartaswan LP ta jihar Kaduna, ta ayyana sunayen waɗanda ta dakatar wanda ya kunshi ɗan takarar mataimakin gwamna a zaben da ya gabata, Bashir Idris Aliyu.
Sauran sun haɗa da ɗan takarar Sanata, Michael Ayuba Auta, da kuma wani babban jigon jam'iyyar a jihar, Ibrahim Sidi Bamali, kamar yadda Dailypost ta rahoto.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Asalin rikicin jam'iyyar LP
Legit.ng Hausa ta tattaro cewa LP ta wayi gari cikin rikicin cikin gida bayan Kotun tarayya mai zama a Abuja ta haramta wa shugaban jam'iyya na ƙasa, Julius Abure, ayyana kansa a matsayin shugaba.
Abure ya yi fatali da umarnin Kotu ya ci gaba da aiki a matsayinsa, hakan ya kawo darewar jam'iyyar gida biyu, inda Lamidi Apapa, ya ware a matsayin sabon shugaban LP.
LP reshen Kaduna bata tare da Apapa
A wata sanarwa da kakakin LP reshen Kaduna, Yusuf Idris, ya fitar bayan taron SEC ranar Asabar, ya ce waɗanda aka dakatar sun halarci taron tsagin Apapa a Bauchi.
A cewar Idris, "Zamu tura matakin da muka ɗauka na dakatar da mutanen uku ga kwamitin gudanarwa na ƙasa (NWC) da sauran masu alhaki domin zartaswa."
Ya ƙara da cewa mambobin jam'iyyar sun kara jaddada mubaya'arsu ga shugaban LP na Kaduna, Honorabul Auwal Tafoki. Ya roki ɗaukacin al'umma su yi watsi da duk wani da ya ayyana kansa a matsayin shugaba.
A wani labarin kuma Tinubu da APC Sun Faɗi Waɗanda Suke Goyon Bayan Su Shugabanci Majalisa Ta 10
Zababben shugaban ƙasa ya ɗauki Sanata Godwill Akpabio a matsayin shugaban majalisar Dattawa, ya kuma ɗauki dan arewa a matsayin kakaki.
Asali: Legit.ng