Sanata Ali Ndume da Barau Jibrin Sun Janye Daga Takarar Shugaban Majalisar Dattawa

Sanata Ali Ndume da Barau Jibrin Sun Janye Daga Takarar Shugaban Majalisar Dattawa

  • Sanatoci biyu daga arewacin Najeriya sun janye daga takarar shugaban majalisar dattawa ta 10
  • Sanata Ali Ndume daga jihar Borno ya ce bayan janyewa zai jagoranci yaƙin neman zaɓen Akpabio wanda Tinubu ke goyon baya
  • Sanata Barau Jibrin daga jihar Kano ya hakura da takara, ya koma mataimaki kamar yadda Tinubu ya tsara

Abuja - Sanata mai wakiltar Borno ta kudu, Sanata Ali Ndume, da Sanata Barau Jibrin daga jihar Kano, sun janye daga takarar kujerar shugaban majalisar dattawa.

Jiga-Jigan sanatocin jam'iyya mai mulki watau APC sun hakura da takara ne jim kaɗan bayan gwamna Dave Umahi na jihar Ebonyi ya janye kuma ya marawa Godwill Akpabio baya.

Sanatocin APC.
Sanata Ali Ndume da Barau Jibrin Sun Janye Daga Takarar Shugaban Majalisar Dattawa Hoto: Sen Barau Jibrin, Muhammad Ali Ndume
Asali: Facebook

A wani taro da ya gudana a gidan gwamnan Ebonyi da ke Abuja, Umahi ya ce ya hakura da takara, kuma ya koma bayan wanda APC ta zaɓa a matsayin ɗan takarar maslaha, kamar yadda The Cable ta rahoto.

Kara karanta wannan

Shugaban Majalisar Dattawa Ta 10: Yari Ya Yi Biris Da Tinubu, Ya Ki Janyewa Akpabio

Legit.ng Hausa ta kawo muku rahoton cewa Tinubu da APC sun amince Akpabio ya zama shugaban majalisar Dattawa, Barau Jibrin kuma mataimakinsa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ndume da Barau sun bi sahun Umahi

Da yake tabbatar da janyewarsa, Sanata Ndume ya ce zai jagorancin yaƙin neman zaben Akpabio a matsayin shugaban majalisar dattawa ta 10 da za'a rantsar a watan Yuni.

Tribune ta rahoto Ndume na cewa:

"Ba janye wa daga takara kaɗai na yi ba, ni zan jagorancin yakin neman zaben Akpabio saboda shi zababben shugaban ƙasa ya marawa baya kuma mun ji mun miƙa wuya domin kishin jam'iyya."
"Asiwaju ya ce ni ya kamata na jagoranci kamfen Akpabio, kun ga yanda ya yi kaurin suna. Saboda haka muna bayan tikitin Akpabio da Barau."

Akpabio ya maida martani

Da yake martani, Akpabio ya ƙara gode wa takwarorinsa bisa goyon bayan burinsa na zama shugaban majalisar dattawa.

Kara karanta wannan

Gwamna Umahi Ya Hakura Da Takarar Kujerar Shugaban Majalisar Dattawa, Ya Ayyana Goyon Bayansa Ga Wani Dan Takara

Ya ce:

"Na miƙa komai ga Allah kuma a koda yaushe na kance In Sha Allah, idan Allah ya so abinda ya tsara ne zai faru a Najeriya."

A wani labarin kuma Hukumar Sojin Najeriya ta bayyana masu hannu a shirin hargitsa bikin rantsar da zabebben shugaban ƙasa.

Hukumar sojin ta ce ta shirya tsaf zata muƙushe duk wanda ya yi yunkurin kawo cikas ranar 29 ga watan Mayu, 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262