"Ba Ka Bi Na Bashin Komai": Wasu Muhimman Abubuwa 5 Da Tinubu Ya Fada Yayin Da Wike Ya Gayyace Shi
Port Harcourt - Gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike dai ya karɓi baƙuncin Bola Tinubu a wata ziyara ta kwana biyu wato jiya Laraba da kuma yau Alhamis a jihar wato 3 da kuma 4 ga watan Mayu.
Da ya ke jawabi a ranar Laraba ga mutanen jihar ta Rivers, zaɓaɓɓen shugaban ƙasar ya yi wasu muhimman jawabai guda 6 da Legit ta naƙalto.
Jawaban sune kamar haka:
Tinubu ya yaba ma uban siyasar jihar Rivers, Peter Odili
A yayin jawabin na shi, Tinubu ya yaba ma Odili wanda ya kira a matsayin aboki, ɗan uwa, mutum mai nagarta, mutum mai daraja sannan kuma mutum mai gina al'umma.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Peter Odili dai tsohon Gwamnan jihar Rivers ne na tsawon tenuwa biyu wato daga 1999 zuwa 2007. Kuma tun daga wancan lokacin zuwa yanzu ana kallon shi a matsayin jagoran siyasar jihar Rivers.
Wike mutum ne mai daɓi'a abar koyi
Tinubu ya jinjina wa Gwamna Wike ya kuma yabe shi da cewar shi mutum ne jajirtacce mai kyakkyawar ɗabi'a, mai son kwatanta adalci musamman ma ganin yadda ya tsayu kan batun tsarin karɓa-karɓa a cikin jam'iyyar sa ba tare da lura da waye abun ba zai ma daɗi ba.
Yanzu lokaci ne na gudanar da shugabanci
Zaɓaɓɓen shugaban ya kuma bayyana cewa lokacin kamfen ya riga da ya wuce, yanzu lokacin gudanar da mulki ne don haka yayi kira ga 'yan adawa da su bar maganar adawa su zo a tafiyar da gwamnati.
A cewar Tinubun:
“Yanzu ba lokacin kamfen bane, lokacin kamfen ya riga da ya wuce, kuzo a gudanar da shugabanci, tunda yanzu lokacin shugabanci ne.”
Bola Tinubu: Cikakken Jerin Gwamnonin APC, PDP Da Suke Tafi Rivers Yayin Da Wike Ya Tarbi Zababben Shugaban Kasa Tinubu
Na ci zaɓe na yanda ya kamata
Tinubu a cikin jawabin na shi ya nuna godiyar shi ga duka 'yan APC da 'yan PDP dangane da goyon bayan da suka bashi wajen ganin ya yi nasara.
Ya ce ya na cikin farin ciki sosai musamman in ya yi duba da irin faɗi tashin da ya yi da kuma irin gwagwarmayar da ya sha wajen ganin ya yi nasara a zaɓen da ya gabata inda daga ƙarshe kuma ya samu nasarar cin zaɓen na shi yanda ya kamata.
Ƙoƙarin ƙulla alaƙa tsakanin jam'iyyu
Tinubu ya bayyana cewa ziyarar da ya kawo jihar ta Rivers na daga cikin burikan shi na ganin cewa ya ƙulla alaƙa da sauran jam'iyyu. Hakan ya yi daidai da ƙudurin Tinubun na kafa gwamnatin haɗaka da ya ke shirin yi idan an rantsar da shi a ofis a 29 ga watan Mayu.
Ba ka bi na bashin komai
Gwamna Wike ya faɗa cikin raha cewa Gwamnatin Tarayya ta biya shi kuɗaɗen gadoji 12 da ya gina domin su ne ya kamata ace sun gina su. Sai Tinubu ya maida mishi martani cikin raha, 'baka bina bashin komi' duk da dai daga baya ya yi bayanin cewa ba shi da ƙarfin yanke wani hukunci yanzu, tunda bai kai ga shiga ofis ba tukun.
Gwamnoni biyar na APC da PDP ne suka raka Tinubu wajen Wike
A wani labari da Legit Hausa ta wallafa, kunji cewa gwamnoni biyar ne ciki kuwa harda na PDP su ka raka Tinubu jihar Rivers domin amsa gayyatar da gwamnan jihar wato Nyesom Wike ya yi mishi.
Gwamnonin sune, Seyi Makinde na jihar Oyo, Badaru Abubakar na Jigawa, Hope Uzodinma na Imo, Dave Umahi na Ebonyi, da kuma Abdulrahman Abdulrazaq na Kwara.
Asali: Legit.ng