An Samu 'Yar Majalisa Mace Ta Fito Takarar Kujera Mai Gwabi a Majalisa
- Ƴar majalisar da ta fito daga jihar Oyo, ta shiga takarar neman mataimakiyar kakakin majalisar wakilai
- Tolulope Akande-Sadipe ta ayyana aniyar ta na neman kujerar mafi girma ta 2 a majalisar ta 10
- Sai dai ƴar majalisar ta ce zata nemi kujerar ne kawai dai jam'iyyar APC ta kai muƙamin zuwa yankin ta
Abuja - Shugabar kwamitin ƴan Najeriya mazauna ƙasashen waje na majalisar wakilai, Tolulope Akande-Sadipe, ta ayyana aniyarta ta neman kujerar mataimakiyar kakakin majalisar wakilai, idan APC ta ba yankin Kudu maso Yamma kujerar.
Premium Times tace da take jawabi ga manema labarai ranar Laraba a birnin tarayya Abuja, Mrs kande-Sadipe, ta bayyana ƙalubalen da ta fuskanta lokacin zaɓe sannan ta yi godiya bisa damar da aka bata ta yiwa al'umma hidima.
Mrs Akande-Sadipe, wacce ita kaɗai ce ƴar majalisar tarayya mace daga jihar Oyo, tace a shirye ta ke ta mayar da hankali kan aikin da ke gabanta sannan ta kawo cigaba a majalisar a matsayin tsintsiya maɗaurin ki ɗaya.
"Abu 1 Mu Ke Jira", Daga Karshe APC Ta Bayyana Dalilin Rashin Fitar Da Tsarin Shugabancin Majalisa Ta 10
A kalamanta:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Ƴan'uwana ƴan majalisa, kamar yadda mu duka mu kayi, na fafata akan tikiti na, mun shiga zaɓe a ranar 25 ga Fabrairu, saɓanin da yawa daga cikin ku, sai da dole aka yi zaɓen cike gurbi da ni a ranar 15 ga Afirilu."
"A dalilin hakan na tsaya gaban ku domin neman goyon bayan ku, a yayin da na fito neman muƙamin mataimakiyar kakakin majalisar tarayya ta 10."
Ta nuna ƙwarin guiwar ta akan damar da ta ke da ita ta yin aikin mataimakiyar kakakin majalisa sannan ta yi alƙawarin yin aiki tuƙuru wajen cimma muradun majalisar, cewar rahoton PM News.
Ta kuma nuna ƙwarin guiwar da ta ke da shi na sauƙe nauyin ayyukan mataimakiyar kakakin majalisar, sannan ta wakilci mazaɓar ta yadda ya dace, idan har jam'iyyar APC ta kai muƙamin yankin Kudu maso Yamma.
APC Ta Bayyana Dalilin Rashin Fitar Da Tsarin Shugabancin Majalisa Ta 10
A wani rahoton na dabamn kuma, kun ji cewa jam'oyyar APC ta bayyana dalilin rashin fitar da yadda za ta raba kujerun majalisa.
Jam'iyyar tace rashin fitar da tsarin na da nasaba da hutun da zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Bola Tinubu, ya tafi ne zuwa ƙasar waje.
Asali: Legit.ng