Daga Karshe APC Ta Bayyana Dalilin Rashin Fitar Da Tsarin Shugabancin Majalisa Ta 10
- Jam'iyyar APC ta fito ta bayyana dalilin samun tsaiko kan fitar da tsarim shugabancin majalisa ta 10
- Shugaban jam'iyyar na ƙasa, Abdullahi Adamu, ya ce rashin Tinubu a ƙasa ne ya kawo mu su tsaiko
- Shugaban ya ce dole sai da zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Bola Tinubu, sannan za su fitar da tsarin shugabancin majalisar
Abuja - Shugaban jam'iyyar All Progressives (APC) na ƙasa, Abdullahi Adamu ya bayyana dalilin da ya sanya har yanzu, jam'iyyar ba ta fitar da tsarin shugabancin majalisa ta 10 ba.
Shugban jam'iyyar ya ce jam'iyyar ta kasa yin taro domin fitar da muƙaman, saboda zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Tinubu, baya nan, cewar rahoton The Cable.
Da ya ke magana da ƴan jarida ranar Laraba a birnin tarayya Abuja, jim kaɗan bayan taron kwamitin gudanarwa na ƙasa na jam'iyyar (NWC), Adamu ya ce jam'iyyar a shirye ta ke ta tafi da kowa wajen yanke hukuncin ta.
A kalamansa:
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
"Lokacin da za mu fitar da tsarin yankunan da shugabannin majalisar za su fito, ba mu kaɗai za mu yi ba. Tsarin za a yi shine tare da wanda yake da iko a ƙasar nan, zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Sanata Bola Tinubu."
"Mu na so ayi tare da shi, ya yi tafiya zuwa ƙasar waje bayan zaɓe, sannan duka satin da ya wuce ya dawo. Sai yana nan yakamata mu fitar da tsarin."
Da ya ke magana a wajen, kakakin jam'iyyar APC na ƙasa, Felix Morka, ya ce jam'iyyar ba sauri ta ke ba ta fitar da tsarin shugabancin majalisar, rahoton New Telegraph.
Morka ya kuma bayyana cewa, an kafa wani kwamiti wanda zai sasanta tsakanin Abdullahi Adamu da mataimakinsa na yankin Arewa ta Yamma, Salihu Lukman.
Jam’iyyun Adawa Sun Yi Taro, An Tsara Yadda Za a Yaki ‘Yan Takaran APC a Majalisa
A wani labarin na daban kuma, jam'iyyun adawa na cigaba da kitsa yadda za su kwace shugabancin majalisa a hannun jam'iyyar APC.
Ƴan majalisun na jam'iyyun adawa, sun yi wani taro inda suka shirya yadda za su shiga takara a neman shugabancin majalisar.
Asali: Legit.ng