"Canji": Buhari Ya Cika Alƙawuran Da Ya Ɗauka, In Ji Fadar Shugaban Ƙasa
- Garba Shehu ya ce Buhari ya tarar da tarin matsaloli da su ka addabi ƙasar a lokacin da ya karɓi mulki
- Ya ce ba adalci ba ne ƙoƙarin ɓata sunan gwamnatin duk da irin ƙoƙarin da ta yi na magance su
- Ya kuma ce an samu cigaba sosai ta ɓangarori da dama irin su ɓangaren tsaro, tattalin arziƙi da kuma matsalar cin hanci
Fadar shugaban ƙasar Najeriya ta bayyana cewa ba adalci ba ne ace duk da irin ƙoƙarin da gwamnatin Shugaba Buhari mai barin gado ta yi ya zamto ana ƙoƙarin muzanta ta hanyar shafa ma ta baƙin fenti.
Babban mai ba wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin watsa labarai kuma mai magana da yawun shugaban ƙasar Malam Garba Shehu ne ya bayyana hakan a cikin wani jawabi da ya gabatar na raddi ga wani gidan jarida a shafin shi na Tuwita.
Ya ce wasu mutane ne ke ƙoƙarin cimma manufofinsu ta hanyar yaɗa maganganu na ɓatanci marasa tushe musamman ma a wannan lokaci da ake ciki na bayan zaɓe wanda ake yawan samun maganganu na tada hankulan jama'a.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Gwamnatin Buhari ta gaji matsaloli masu ɗumbin yawa kuma ta magance su
A rahoton da Daily Trust ta wallafa, Garba Shehu ya bayyana cewa gwamnatin Buhari ta gaji tarin matsaloli irin su matsalar cin hanci da rashawa da ta yi ma ƙasar katutu, matsalar 'yan ta'addan Boko haram, da kuma matsalar karyewar farashin mai a kasuwar duniya.
Ya bayyana cewa matsalar Boko haram yanzu ta kau, tunda a yanzu haka babu sauran wani yanki da yake a hannun su, jami'an tsaro sun riga da sun murƙushe su da su da duk shuwagabannin na su.
Garba Shehu ya ce:
“Matsalar cin hanci da rashawa ma an yi mata babbar illa, musamman ma da gwamnatin Buhari ta fito da tsarin masu fasa ƙwai da ta ba wa 'yan Najeriya damar kawo rahoton dukiya da su ka ga wasu 'yan siyasa sun sata ba tare da fargaba ba, wanda ta hakan an samu damar ƙwato biliyoyin kuɗaɗe da aka ɓoye a bankunan ƙasashen ƙetare.”
An samu haɓakar tattalin arziƙin ƙasa a mulkin Buhari
Shehu ya kuma ƙara da cewar tattalin arziƙin ƙasa ma ya samu ci gaba, tun da Buhari ya karɓi mulki. Ya ce asusun ajiyar Najeriya na ƙasar waje ma ya ci gaba da ɓunƙasa a shekaru takwas ɗin mulkin Buhari. Sannan a cikin shekaru biyu na farkon mulkin shi an samu damar ninka abinda ake fitarwa waje na kayan noma.
Fadar shugaban ƙasa ta kuma ƙara da cewa gwamnatin shugaba Buhari ta taimaki gami da ɗaga darajar rayuwar 'yan Najeriya da dama.
Ya ce akwai tsarin tallafin bayar da kuɗi ga magidanta masu ƙaramin ƙarfi su 355,000 da ake ba wa kowane N10,000 sau biyu a wata. Haka nan ma akwai tsarin tallafi da aka ba wa waɗanda su ke cikin hali na buƙata N20,000 kowane a cikin jihohi 36 na ƙasar nan da ma birnin tarayya.
Ni ba mai laifi bane, har sai kotu ta ayyana hakan - Doguwa
A wani labarin kuma, ɗan majalisa mai wakiltar Doguwa da Tudun Wada jihar Kano Alhassan Ado Doguwa ya bayyana cewa shi fa ba mai laifi ba ne tunda kotu ba ta tabbatar da hakan ba.
Ya yi wannan jawabi ne a zauren majalisa a yayin da ya ke bayyana aniyar shi ta neman kujerar shugabancin majalisar wakilai ta 10 da ake ta shirye-shiryen gabatarwa.
Asali: Legit.ng