Babban Abin Nadama a Mulkin Buhari Da Zai Kare 29 Ga Watan Mayu, Galadima

Babban Abin Nadama a Mulkin Buhari Da Zai Kare 29 Ga Watan Mayu, Galadima

  • Buba Galadima, tsohon makusancin shugaba Buhari ya bayyana abu biyu da ya kira babban abin nadama a mulkin Buhari
  • Jigon jam'iyyar NNPP mai kayan marmari ya ce abun da takaici yadda Buhari zai bar mulki bayan dabaibaye siyasa da akidar Addini da kuɗi
  • Ya ce a yanzu cancanta ko gogewarka a aiki ba zai baka nasara a zaɓe ba, amma idan kana da kuɗi magana ta ƙare

Abuja - Tsohon makusancin shugaba Muhammadu Buhari kuma jigon jam'iyyar NNPP, Buba Galadima, ya bayyana babban abin nadama a wannan mulkin da zai ƙare ranar 29 ga watan Mayu, 2023.

Jigon jam'iyyar New Nigeria Peoples Party watau NNPP mai kayan marmari ya ce Buhari zai miƙa mulki bayan ya gurbata tsarin siyasa da abu guda biyu, inji rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Zabin Tinubu a Shugabancin Majalisar Dattawa Ya Yi Kus-Kus da Shugaba Buhari, Bayanai Sun Bayyana

Buba Galadima.
Babban Abin Nadama a Mulkin Buhari Da Zai Kare 29 Ga Watan Mayu, Galadima Hoto: Buba Galadima
Asali: UGC

Galadima ya yi ikirarin cewa babban abin nadama shi ne Buhari zai sauka ya bar siyasar Najeriya ta koma nuna Addini da kuma ƙarfin kuɗi.

Tsohon makusancin shugaban kasan ya faɗi haka yayin da yake jawabi a wata hira da Arise TV ranar Litinin 1 ga watan Mayu, 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Idan baku manta ba, ana tsammanin shugaban kasa, Muhammadu Buhari, zai miƙa ragamar mulki ga zababben shugaban kasa kuma magajinsa, Asiwaju Bola Tinubu, ranar 29 ga watan Mayu, 2023.

Tinubu ya samu nasarar zama zababben shugaban kasa bayan lallasa manyan abokan karawarsa, Atiku Abubakar, na PDP da Peter Obi na Labour Party, ranar 25 ga watan Fabrairu, 2023.

Da yake tsokaci kan gwamnatin shugaban ƙasa mai barin gado, Muhammadu Buhari, Buba Galadima ya ce:

"Babban abinda na yi nadama a ƙasar nan shi ne Buhari ya sauya akalar siyasar Najeriya ta koma aƙidar addini da kuma batu na kuɗi."

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Yari Ya Gana Da Buhari, Ya Ce Arewa Ta Cancanci Shugabancin Majalisar Dattawa

"Wannan sun fi maguɗin zabe muni saboda a yanzu ba zaka iya cin zaɓe bisa gogewarka a aiki ba."
Cancanta, aikin da ka yi wa al'umma ko wasu ayyukan Alherin da aka yi duk ba zasu sanya ka ci zaɓe ba. Amma abinda zai sa ka yi nasara cikin sauki shi ne kuɗi."

Ko Sisin Kwabo Ban Karba Don Ayyana Aishatu Binani a Matsayin Gwamna Ba, Ari

A wani labarin kuma Tsohon kwamishinan zabe a jihar Adamawa Ya Fayyace gaskiya kan zargin an ba shi cin hancin biliyan N2bn

Barista Hudu Yunusa Ari, ya ja hankalin Najeriya baki ɗaya bayan ayyana Sanata Aishatu Binani a matsayin wacce ta lashe zaben gwamna a Adamawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262