Mambobi 18 Sun Tsige Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Abia, Sun Nada Sabo

Mambobi 18 Sun Tsige Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Abia, Sun Nada Sabo

  • Majalisar dokokin jihar Abiya ta shiga rikici bayan mambobi 18 cikin 27 sun zauna sun tsige kakakin majalisa
  • Yan majalisun sun zargi Honorabul Chinedum Orji da rashin ladabi don haka suka yanke raba shi da muƙaminsa
  • Wata majiya daga fadar gwamnatin Abiya ta ce yan majlisun sun yi aikin banza tunda ba'a zauren majalisa suka ɗauki matakin ba

Abia - Mambobin majalisar dokokin jihar Abiya sun kaɗa kuri'ar tsige kakakin majalisar, Honorabul Chinedum Orji.

Mambobi 18 daga cikin 27 na majalisar dokokin ne suka amince da tsige shugaban majalisar yayin wani zaman gaggawa da suka yi a wani wuri da basu bayyana ba.

Chinedum Orji
Mambobi 18 Sun Tsige Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Abia, Sun Nada Sabo Hoto: channelstv
Asali: UGC

Channels tv ta tattaro cewa mamban majalisar, Chukwudi Apugo, mai wakiltar mazabar Umuahia ta gabas a inuwar jam'iyyar PDP ne ya gabatar da kudirin tunbuke kakakin.

Kara karanta wannan

‘Dan Majalisar Kano da Ake Zargi da Kisan Kai Ya Fito Takarar Shugaban Majalisa

Bayan haka ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Umunneochia a majalisar dokokin Abiya, Okey Igwe, na jam'iyyar PDP, ya goyi bayan kudirin nan take.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Meyasa suka yanke tunbuke kakakin majalisa?

Game da dalilin ɗaukar wannan matakin, yan majalisun sun zargi tsohon shugaban majalisar da rashin ladabi da kuma girman kai da nuna yafi kowa.

Amma wata majiya mai kusanci da gidan gwamnatin jihar Abiya ta ayyana tsige kakakin majalisar da, "Wasan kwaikwayon majalisar dokoki," wanda ba zai kai labari ba.

A cewar majiyar, zauren majalisar dokoki na kulle kuma an sanya kwaɗo shiyasa mambobin ba yadda suka iya sai dai suka nemi wani wurin suka zauna.

Bisa haka majiyar ta bayyana cewa duk wani mataki da mambobin 18 suna ɗauka a wani wuri daban ba zauren majalisa ba, bai da amfani kuma ba zai hau wuyan kakaki ba.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Yari Ya Gana Da Buhari, Ya Ce Arewa Ta Cancanci Shugabancin Majalisar Dattawa

Shin yan majalisar sun zabi sabon kakaki?

Sai dai bayanai sun nuna cewa magatakardan majalisar baya nan lokacin da mambobin suka tsige kakakin ballantana ya rantsar da sabon shugaban da suka zaɓa, Guardian ta rahoto.

A wani labarin kuma Kwamishinan Zaben Adamawa, Hudu Ari, Ya Shiga Hannun Yan Sanda A Abuja

Jami'an rundunar yan sanda sun damƙe tsohon kwamishinan zaben Adamawa, Hudu Ari, sun titsiye shi kan ayyana Aishatu Binani.

Sufeta Janar na yan sandan ƙasar nan ya tabbatar da cewa babu wani shafaffe da mai, duk mai hannu a lamarin sai doka ta hukunta shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262