Kwamishinan Zaben Adamawa, Hudu Ari, Ya Shiga Hannun Yan Sanda
- Rundunar 'yan sandan Najeriya ta kama tsohon kwamishinan hukumar zabe (REC) na jihar Adamawa, Hudu Ari
- A wata sanarwa da jami'in hulda da jama'a ya fitar, ya ce 'yan sanda sun cafke Barista Ari ranar Talata a Abuja
- IGP Usman Baba ya tabbatar da cewa duk wani mai hannu a lamarin zai girbi abinda ya shuka a gaban Kotu
Abuja - Dakataccen kwamishinan hukumar zaɓe (REC) na jihar Adamawa, Barista Hudu Yunusa Ari, ya shiga hannun rundunar yan sandan Najeriya.
Wata majiya daga cikin jami'an hukumar yan sanda ta tabbatarwa Channels tv ta wayar salula, ranar Talata cewa, tsohon kwamishinan na tsare a hannunsu.
Wannan ci gaban na zuwa ne awanni kaɗan bayan Hudu Ari, a wata hira da BBC Hausa, ya ce ya shirya miƙa kansa ga 'yan sanda, mako biyu kenan bayan ya yi layar zana.
Shugaban Hukumar Tsaro a Jihar Arewa Ya Tsallake Rijiya Da Baya a Hannun 'Yan Bindiga, Cikakkun Bayanai Sun Bayyana
Mun cafke Hudu Ari a Abuja - NPF
A wata sanarwa da jami'in hulɗa da jama'a na rundunar yan sandan Najeriya, Muyiwa Adejobi, ya fitar, ya ce rundunar ta damƙe Hudu Ari a Abuja ranar Talata.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A rahoton Daily Trust, Adejobi ya ce:
"Barista Ari, wanda tawagar dakarun yan sanda masu shirye-shirye, sa ido da binciken harkokin da suka shafi zaɓe suka cafke a Abuja ranar Talata 2 ga watan Mayu, 2023, yana tsare yanzu haka."
"Kuma sun titsiye shi kan abinda ya ba shi kwarin guiwa har ya yi wa doka hawan ƙawara yayin cikon zaben gwamna a jihar Adamawa."
"Bugu da ƙari, duk wani jami'in hukumar INEC da ɗaidaikun mutane da ake zargin suna da hannu a lamarin, suna hannun tawagar ana gudanar da bincike."
Kakakin yan sandan ya ce Sufetan yan sanda na ƙasa ya tabbatar da cewa zai sa a kamo duk mai hannu a badaƙalar kuma a tuhumesa kamar yadda doka ta tanadar.
"IGP ya tabbatar da shirin rundunar 'yan sanda na ganin gaskiya ta yi halinta kuma duk mai hannu ya girbi abinda ya shuka a gaban ƙuliya."
Ko Sisin Kwabo Bar Karba Don Ayyana Aishatu Binani a Matsayin Gwamna Ba, Ari
A wani labarin kuma Dakataccen kwamishinan Zaben Adamawa, Hudu Ari, ya fayyace gaskiya kan jita-jitar ya karbi cin hancin N2bn
A wata hira da safiyar Talata, Barista Ari, ya ce ba shi da alaƙa da Aishatu Binani ko gwamna Ahmadu Fintiri kuma bai karbi ko sisin kwabo ba.
Haka zalika ya ce bai yi nadamar ayyana Sanata Aishatu Binani a matsayin wacce ta lashe zaben gwamna ba domin a kan gaskiya yake.
Asali: Legit.ng