Gwamnan APC Ya Maida Martani Kan Rahoton Kaiwa Ayarinsa Hari da Kashe Yan Sanda
- Gwamnan Imo da ke kudu maso gabashin Najeriya ya musanta rahoton cewa an farmaki Ayarinsa
- Hope Uzodinma, mamban jam'iyyar APC, ya ce rahoton aikin yan adawa ne waɗanda ke kokarin ganin bayansa
- Ranar 11 ga watan Nuwamba, 2023, INEC zata gudanar da zaben gwamna a Imo kuma Uzodinma yana neman tazarce a inuwar APC
Imo - Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo ya musanta rahoton dake yawo wanda ya yi ikirarin cewa 'yan bindiga sun farmaki ayarin motocinsa, sun sheƙe yan sanda 7.
Premium Times ta ce rahoton ya yi ikirarin cewa 'yan bindigan sun kaiwa ayarin gwamnan hari a Titin Ngor Okpala-Aba da ke jihar Imo ranar Asabar.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Oguwike Nwachuku, ya fitar da yammacin Asabar, Uzodinma, ya ce babu wanda ya farmaki ayarinsa.
Gwamna Uzodinma ya ayyana rahoton da aikin sheɗanci kuma kirkirarrar ƙarya mara tushe balle makama.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Ayarin gwamna Uzodinma bai je ko ina ba ranar Asabar saboda babu buƙatar hakan domin ayyuka sun yi wa mai girma gwamna yawa a Ofishinsa tun da safe har kawo yannzu da yamma."
"Yana kan duba batutuwan da suka shafi jihar Imo waɗanda zauciyarsa ta ke ƙauna kuma masu amfani ga talakawan jiharsa," inji Sanarwan.
Gwamna Uzodinma, mamban jam'iyyar APC, ya zargi 'ya'yan jam'iyyun adawa da hannu a kirkirar wannan rahoton ƙanzon kuregen, "Domin su wargaza shi."
Gwamna Uzodinma ya bayyana masu hannu a matsalar tsaro
Hope Uzodinma ya ƙara maimaita zargin da yake wa wasu 'yan adawa da bai ambaci sunansu ba, waɗanda ya kira su da makiyan gwamnatinsa, masu hannu a tabarbarewar tsaron Imo.
"Ba su haƙura da mummunan nufinsu ba saboda sun gaza kamo ko da kafar nasarorin da gwamna ya samu duk makircin da suka kulla na ɓata sunan gwamnatinsa."
"Labari mai daɗin shi ne har yanzu gwamna Uzodinma na nan kan bakarsa na sauya akalar jihar Imo zuwa turba mai kyau kuma zai ci gaba da haka matuƙar yana kan kujerar gwamna."
Interpol ta tsoma baki a zaben Adamawa
A wani labarin kuma Kwamishinan Zaben Adamawa Ya Ƙara Shiga Sabon Tasku Kan Ayyana Aishatu Binani
Hukumar yan sandan ƙasa ta ƙasa sun gayyaci dakataccen kwamishinan zaben jihar Adamawa, Barista Yunusa Hudu Ari, kan abinda ya aikata lokacin zaɓe.
Asali: Legit.ng