Gwamnatin Tarayya Ta Zargi El-Rufai da Jefa Rayuwar Wasu Daliban Kaduna Cikin Hadari

Gwamnatin Tarayya Ta Zargi El-Rufai da Jefa Rayuwar Wasu Daliban Kaduna Cikin Hadari

  • Ana zargin Gwamnatin jihar Kaduna da shiga makarantar FGC Malali har ta ruguza mata katanga
  • A dalilin haka aka ji wasu jami’an gwamnatin tarayya sun yi karar gwamnatin Nasir El-Rufai a kotu
  • Rusa makarantar ta saba doka, sannan ana ikirarin haka zai fallasa dalibai da malamai ga rashin tsaro

Abuja - Gwamnatin tarayya a Najeriya ta fito ta na mai zargin Gwamnatin jihar Kaduna da Nasir El-Rufai yake jagoranta da wasa da ran jama’a.

Sun ta ce Gwamnatin ta na tuhumar Mai girma Malam Nasir El-Rufai da jefa daliban da ke karatu a makarantar gwamnatin FGC Malali a cikin hadari.

Wani babban jami’in gwamnatin Najeriya ya zanta da ‘yan jarida a garin Abuja a karshen makon nan, inda ya koka a kan halin da ake ciki a Kaduna.

Jami’in yake cewa gwamnatin jihar Kaduna ta aukawa makarantar FGC Malali, ta ruguza wani bangare na katangar da ke kare ma’aikata da dalibai.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali Yayin Da Aka Yi Wa Wasu Matasa Biyu Yankan Rago a Jihar Filato

Magana ta kai ga IGP

Ganin halin rashin tsaro da ake fama da shi a yanzu, majiyar ta ce gwamnatin tarayya ta aikawa Sufeta Janar na ‘Yan sanda takarda a kan batun.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton ya ce an umarci Shugaban ‘Yan sanda da ya aika dakaru domin su yi gadin makarantar.

Gwamnatin Kaduna
Gwamna Nasir El-Rufai Hoto: @GovKaduna
Asali: Twitter

A wasikar da aka aikawa IGP, an sanar da shi cewa kwana daya da Hukumar KASUPDA ta aiko takarda zuwa makarantar, aka ruguza katangarta.

A ranar 19 ga watan Afrilu, jami’an KASUPDA suka shiga makarantar Malali, su ka shiga rusa katangarta da karfi da yaji, sai aka fara daura wani ginin.

Vanguard ta ce abin ban tsoron shi ne a ranar Lahadin da ta wuce dalibai za su dawo daga hutu, wasikar ta ce bai dace daliban su ci karo da wannan ba.

Kara karanta wannan

Lauje cikin nadi: Shehu Sani ya tona asirin Buhari, ya fadi gaskiyar dalilin dage kidaya

Za a tafi kotu

Baya ga haka, an shigar da karar gwamnatin Kaduna a kotu, ana neman Alkali ya haramtawa Gwamna El-Rufai cigaba da shiga makarantar tarayyar.

Zuwa yanzu ba a sa lokacin da kotu za ta saurari shari’ar ba. Ba wannan ne karon farko da aka yi karar gwamnatin Malam El-Rufai a dalilin rikicin fili ba.

Tsige Muhammadu Sanusi II

Da yake magana a dandalin Twitter, an ji labari 'dan Sarkin Kano na 14, Muhammadu Sanusi II ya ce duk jihar babu masanin tattalin arziki irin mahaifinsa.

A karshen makon nan wani ya tambayi ko me ya jawo aka tunbuke Sanusi Lamido Sanusi, a nan Adam Sanusi ya ce zunubin Sanusi shi ne sukar gwamnati.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng